Jump to content

Wq/ha/William Shakespeare

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > William Shakespeare
Duka duniya fage ce, sannan kuma dukkannin maza da mata sun kasance ‘yan wasa ne kawai:
Suna da kofofin fita da na shiga; sannan kuma mutum daya a lokacinsa yakan taka rawa a ɓangarori da dama…
~ Jaques a cikin Kamar Yadda Kake So
Laifin ya kai Brutus, ba ya a cikin taurarin mu, Sai dai a gare mu, cewa mun kasance Underlings. Cassius, Act I, scene ii.

William Shakespeare (26 April 1564 (baptiza) – 23 April 1616), ya kasance mawaki ne dan kasa Ingila, marubucin wasanni kuma dan wasan kwaikwaiyo, wanda ake dauka a matsayin marubucin harshen Turanci da yafi kowa fice, kuma dan wasan dirama da yafi kowa a duniya.

Maganganu

[edit | edit source]
Nasarar zamani shine ya natsar da sarakuna masu jayayya,
Ta fito da karya fili, sannan ta kawo gaskiya zuwa haske.
Albarka su tabbata ga mutumin da ya sauƙaƙawa waɗannan duwatsu
Sannan tsinuwa sun tabbata ga wanda ya matsar da ƙasusuwa na.
  • Duk abinda ba za’a iya watsi da shi ba dole a rungume shi.
  • Kyawu da kanshi kan jawo hankali
    Na idanun maza ba sai da mai jawabi ba.
  • Nasarar zamani shine ya natsar da sarakuna masu jayayya,
    Ya fito da karya fili, sannan ya kawo gaskiya zuwa haske.
    • The Rape of Lucrece.
  • Yarinta da tsufa bazasu taba rayuwa tare ba
    Yarinta na cike da nishadi, tsufa na cike da kula wa.
    • The Passionate Pilgrim: A Madrigal; akwai dan kokwanto game da wanda ya kirkiro wannan.


  • Menene acikin suna? Wanda muke kira da rose,
    daga nan duk wani suna zai yi daɗi.
    • Juliet, Act II, scene ii.