Wq/ha/Willa Cather
Appearance
Willa Sibert Cather (7 Disemba 1873 – 24 Afurelu 1947), tana daga shahararrun marubuta nobel ‘yar Amurka, wacce tayi fice da nuna rayuwar mutanen Amurka a cikin littattafan ta.
Zantuka
[edit | edit source]- Babu wanda zai gina tsaronsa akan karimcin wani mutum. Mutum biyu idan suna kaunar juna, zasu girma tare a bukatunsu, dabi’u da alfahari, amma kuma halayensu na rayuwa (ko da kuwa me muke nufi da hakan) basu taba zama daya. Tushen da mutum ya taso da shi shine tushe, kuma mai karamci mai karamci ne, har karshe.
- Alexander's Bridge (1912) Ch. 8
- Babu wani abu mafi hadari kaman zaman banza. Rayuwa daya kawai kake da shi, samartaka daya, kuma zaka iya barin shi ya sullube ta yatsunka idan kana so; babu wani abu da yafi hakan sauki. Mutane da yawa hakan suke yi.
- One of Ours (1922), Bk. II, Ch. 6
- Bai taka kara ya karya ba ko da wa muke rayuwa da shi a wannan rayuwa. Amma yana da muhimmanci sosai wanda muke mafarkin sa.
- Youth and the Bright Medusa, "A Gold Slipper" (1920)
- Watakila matattu na kokarin yiwa rayayyu magana kamar yadda tsofaffi ke ga yara.
- One of Ours (1922), Bk. II, Ch. 6