Jump to content

Wq/ha/Veronica Chambers

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Veronica Chambers
Veronica Chambers a 2017

Veronica Chambers bakar fatar Latin ce wacce daga mafaran rubuce-rubuce kuma babbar ’yar jarida, marubuciyar nobel, marubuciyar insha’i, mai koyarwa kuma mai kirkirar muhalla.

Zantuka[edit | edit source]

  • Na kasance mace ta farko edita a gidan mujallar New York Times. Ya kasance abun mamaki! Ni ba wata tsohuwa bace balle ka ce zan zamo ta farko a wani abu a gida Mujallar New York Times, amma na zamo… Mutane suna so su san abubuwa, sukan yi tambaya akan gashi na, suna so su san daga ina nike, suna so su san idan hip hop kadai nike saurare. Idan mutane basu saba da bambanci ba, akwai nauyi na tambayoyi da yawa da zaka amsa…
  • Na ji dadi da Camilla ta fara ganowa. Muna fadawa yara cewa babu tambaya mara amfani. Amma idan aka jefa wariyar launin fata a tsakani, akwai tambayoyi da dama - wasu suna da zafi a tambaya, wasu suna da zafi wajen amsawa kuma mu duka muna fadar kalaman shirme wani lokacin. Ina tsammanin idan masu karatu suka karanta labarin Camilla cewa ba wai akan lokacin guda daya bane ko haduwa daya, a kan tsayawa da dakakken zuciya ne da cigaba da tafiya gaba. Kamar yadda Maya Angelou takan ce, idan ka sani yadda ya dace, zaka yi yadda ya dace.