Wq/ha/Siddhartha Gautama
Siddhārtha Gautama (Sanskrit/Devanagari: सिद्धार्थ गौतम Siddhārtha Gautama, c. 563/624 – c. 483/544 BCE) ko kuma Siddhattha Gotama a yaren Pali,; sannan kuma ana kiransa da Gautama Buddha, Shakyamuni Buddha ("Buddha, Sage na Shakyas") ko kuma a saukake Buddha, ya kasance sufi, masanin falsafa kuma mai koyarwa, jagorar addini wanda ta shi ne aka samo addinin Buddizanci. Anyi imanin, cewa yayi rayuwa kuma ya koyar a yankin arewa maso gabashin Tshohuwar Indiya a wani lokaci a tsakanin karni na 6th da na 4th BCE.
Zantuka
[edit | edit source]Pali Canon Sutta Pitaka Akwai wadannan hanyoyi hudu na amsa tambayoyi. Wadanne hudu? Akwai tambayoyin da ake amsa su a rarrabe [kai tsaye eh, a'a, wannan, wancan]. Akwai kuma tambayoyin da ake amsa wa a cikin salo (cikin kwarewa) amsa ta hanyar [yin bayani da sake maimaita bayani akan abubuwa]. Akwai tambayoyin da ake amsa su ta hanyar wata tambayan. Akwai kuma tambayoyin da ake ture su gefe. Wadannan sune hanyoyi guda hudu na amsa tambaya. Kamar yadda aka hakayo a cikin littafin Ṭhānissaro (Bhikkhu.) ( shekara ta 2004) Handful of leaves. Vol. 3, p. 80