Jump to content

Wq/ha/Shona Brown

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Shona Brown
Shona Brown, 2007

Shona Lesley Brown (an haife ta ca. 1960), ‘yar kasuwa ce ‘yar Amurka kuma mai bada shawarwar ga masana’antu masu zaman kansu da kamfanoni. Ma’akaciyar Google ce na tsawon lokaci, na baya bayan nan ta kasance babbar mataimakiyar shugaban kamfanin fannin kasuwanci a shekara ta 2012, kafin ta yi murabus ta zamo mai bada shawara ga kamfanin.

Zantuka[edit | edit source]

Competing on the Edge, 1998[edit | edit source]

  • Manajoji da suke shirya gaba sosai kan same shi ba daidai ba. Wata sa’in sukan iso kasuwa da wuri da yawa a dalilin haka sai sun jira bukata ya tashi kafin su sayar. Wani lokacin suna zuwa cikin latti a dalilin hakan sai sunyi hanzari don su isa.
    • p. 135