Jump to content

Wq/ha/Shenaaz El-Halabi

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Shenaaz El-Halabi

Shenaaz El-Halabi tsohuwar Sakatariyar Lafiya da Jindadi ce ta dundundun. Ta ajiye aiki a ranar 30 Nuwamba 2017 don yin aiki tare da Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) bayan ta yi aiki a ma’aikatar na tsawon shekaru 24..

Zantuka

[edit | edit source]
  • Ilimantar da mata don daukar lafiyayyar rayuwa ta hanyar daukar binciken lafiya ta cancer don rage cigaban sababbin matsaloli, da kuma binciko sababbin cututtuka wanda za’a iya magance su.
  • Kariya shine mafi muhimmanci a Botswana, samar da bayanai ga mutane wanda zai amfane su don kada su fada wa al’amura masu hadari. Shawarar itace fara lafiyayyar rayuwa tun daga yarinta.
  • Kiwon lafiya shine makullin baunkasar tattalin arziki da cigaba. Ga masu saka hannun jari, Botswana suna samar da amincin siyasa, sadaukarwa, lissafi da kuma albarkar kudi.
  • Ina so in bunkasa kariya; in tabbatar da cigaba, kiwon lafiya mai inganci; kuma in samar da salon kiwon lafiya na duniya.