Wq/ha/Saratu Gidado
Appearance
Saratu Gidado, (an haife ta a ranan 17 ga watan Janairu shekarata 1968), wacce aka fi sani da Daso, ‘yar wasan fina-finan Najeriya ce, musamman a masana’antar fina-finan Kannywood. Ta rasu a ranar 9 ga watan Afurelu 2024.[1]
Zantuttuka
[edit | edit source]- Zan shawarci sabbin ‘yan Kannywood, musamman mata, cewa a zamaninmu ba mu sha kwaya ko barasa. A kwanakin nan, mutunta ya ragu kuma akwai kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi da barasa da ke shafar mu duka. Don haka su ji tsoron Allah su sani al’umma na kallonmu. "Me ya sa nake son taka rawar mugayen mata - Daso", Blueprint (Agusta 27, 2021)