Wq/ha/Nana Aisha
Nana Aisha ɗaya ce daga cikin Matan Annabi Muhammad Saw.Wacce akeyi Mata laƙabi da uwar muminai, Nana Aisha ta taka muhimmiyar rawa a farkon tarihin Musulunci, a lokacin rayuwar Annabi Muhammadu Saw da kuma bayan rasuwarsa. A al’adar Ahlus- Sunnah, ana zaton A’isha ta kasance mai ilimi da bincike. Ta ba da gudummawa wajen yaɗa sakon Annabi Muhammad tare da yi wa al’ummar Musulmi hidima na tsawon shekaru 44 bayan rasuwarsa. Ita kuma ta shahara wajen ruwaito hadisai 2210, ba wai kawai a kan abubuwan da suka shafi rayuwar Annabi ba, har ma da batutuwa kamar gado, hajji, da fiyayyen halitta. Hankalinta da iliminta a fannoni daban-daban da suka haɗa da wake-wake da likitanci, sun samu yabo matuka daga wajen fitattun malamai na farko irin su al- Zuhuri da ɗalibarta Urwa bn al- Zubair.
Zantuttuka
Mutane ba su kula da mafi kyawun aikin ibada: Tawali'u.
• Ibn Abee Shaybah ya tattara (13/360) Ibn Hajr ya sanya wannan Athar a matsayin Saheeh.
cikin Hadisi
• An karbo daga A’isha (uwar muminai) ta ce: “Al- Harith bin Hisham ya tambayi Manzon Allah “Ya Manzon Allah! Ta yaya aka saukar da wahayi zuwa gare ka? Sai Manzon Allah (saww) ya karva masa da cewa: “Wani lokaci yakan kasance (sauya) kamar qarar qararrawa, wannan nau’i na ilhami shi ne ya fi komai wuya sai wannan hali ya wuce bayan na riqe abin da aka yi masa wahayi. mutum da magana da ni kuma na gane duk abin da ya ce." Nana A’isha ta kara da cewa: Lallai na ga Annabi (SAWA) ana yi masa wahayi a rana mai tsananin sanyi, sai na ga gumi na fita daga goshinsa (yayin da wahayi ya kare).