Wq/ha/Muhammadu Buhari

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Muhammadu Buhari
Shugaban Ƙasar Najeriya, Muhammad Buhari.

Muhammadu Buhari ya kasance shugaban kasar Najeriya (na farar hula) tun daga shekara ta 2015 har yi zuwa yau, sannan kuma tsohon shugaban kasa na mulkin soja.

Kalaman Hikima[edit | edit source]

  • Nayi rantsuwa da Littafi mai Tsarki 'yan mintuna da suka wuce, na yi niyyar cika alƙawarin da na ɗauka akan zan zamo shugaba ga ɗaukakin al'ummar Najeriya.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 22 August 2022.
  • Ni na kowa ne sannan kuma Ni ba mallakin kowa bane.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 22 August 2022.
  • Wasu mutane suna yaɗa jita-jita na tsoratarwa akan akan cewa idan na koma kan kujera ta zan bi-biye su. Wannan. Waɗannan zantuka basu da tushe. Babu maida martani. Abin da ya wuce ya wuce.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 23 August 2022.
  • Maƙwabtanmu na yankunan Afurka su tabbata da cewa, Najeriya a ƙarƙashin mulkinmu zata taka duk wata rawa ta shugabanci da Nahiyar Afirka ke tsammani daga gare ta. Zanyi amfani da wannan dama wajen miƙa godiya ga gwamnatocin kasashen Kamaru, Chadi da kuma Niger da jajircewa da sojojinsu a wajen yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a Najeriya.
    • "Nigeria President Muhammadu Buhari's Inauguration Address". Council on Foreign Relations. Retrieved 2022-08-22.
  • Har wayau, inaso in ƙara tabbatar wa duniya da cewa a shirye muke da mu bada haɗin-kai kuma mu taimaka wajen yaƙi da duk wata barazana da ke tasowa na ta'addanci a yankunan iyakokin kasashe.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 23 August 2022.
  • A nan gida (Najeriya) muna fama da matsaloli. Rashin tsaro da cin-hanci da rashawa da suka yi mana ƙatutu wanda babu ranar kawo ƙarshensu da kuma abin al'ajabi na ƙarancin man-fetur da wutar lantarki na daga cikin abubuwan da suke buƙatar kulawa.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 23 August 2022.
  • Acikin 'yan lokutan nan (wasu) shuwagabannin Najeriya sun saɓa manufarmu. Iyayenmu, kamar su Mr Herbert Macauley, Dr Nnamdi Azikiwe, Chief Obafemi Awolowo, Alhaji Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto), Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, Malam Aminu Kano, Chief J.S. Tarka, Mr Eyo Ita, Chief Denis Osadeby, Chief Ladoke Akintola da makamantansu sunyi aiki tuƙuru wajen gina gwamnati mai tsari. Wataƙila salonsu sun bambanta ta fuskar tsari, dabaru da kuma bayanai, amma kansu haɗe yake wajen gina kasa mai zaman kanta da kuma nasarorinta. Wasu daga cikin waɗanda suka gajesu suna nuna halaye irin na ƙananan yara suna lalata komai kuma suna haifar da rashin tsari a cikin gida.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 23 August 2022.
  • Bugu da ƙari, mu 'yan Najeriya kada mu manta da cewa mu jikokine na al'ummomi masu girman nasaba: Halifancin Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo, Daular Masarautar Kanem Borno, Daular Masarautar Oyo, Daular Masarautar Benin da kuma Masarautar Sarki Jaja. Jinin waɗannn kakanni namu masu daraja suna yawo acikin jijiyoyin jikinmu. Abunda ya rage a yanzu shine mu gina akan waɗannan abubuwan gado da suka bar mana, wajen zamanantarwa da kuma daukaka Najeriya.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 23 August 2022.
  • Duk da rashin ƙarfin guiwa, hakan ba yana nufin cewa baza'a iya shawo kansu bane. A yanzu akwai yarjejeniya ta ƙasa, cewa hanyar da muka zaɓa wajen gina ƙasarmu itace dimukraɗiya. Domin cimma waɗannan ƙudirorin, dole sai mun farka wajen aiwatar da tsarin dimukraɗiya. Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin kulawa ta baza tayi yinƙurin yin shisshigi acikin ayyukan Majalisa Dokoki ko Sashen Shari'a ba. Waɗanda ke da alhakin tabbatar da tsaro zasuyi aiki dangane da kundin tsarin mulki ta ƙasa. Zamu sake gina sashen ma'aikatan gwamnati muyi mata garambawul, don ta ƙara tasiri da kuma hidima. Zamu kuma cajesu da su sanya gaskiya da riƙon amana acikin ayyukansu don daidaita tsarin.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 23 August 2022.
  • Dangane da sashin Majalisa dole ne su cika haƙƙoƙinsu wajen tabbatar da dokoki, su riƙa yin aiki na hangen nesa acikin salo na haɗin kai. Sashin shari'a kuwa dole ne ta tuba ta kuma wanke kanta daga zunubanta da suka wuce. Ƙasarmu a yau tana buƙatar sashin shari'a da suyi aiki tare da ɗaukan mataki akan harkoki musamman waɗanda suka shafi cin hanci da rashawa, tsananin rashin gaskiya akan dukiya ko kuma ko danne hakkin al'umma. Sai idan waɗannan rassa guda uku sunyi aiki dangane da tsarin mulki ne gwamnati zata iya samun daman yi wa ƙasa hidima cikin jindadi da kuma kauce wa ruɗani dake mamaye mulkinmu a yau.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 23 August 2022.
  • A koda yaushe, ya ci ace an fayyace dangantakar dake tsakanin Abuja da sauran Jihohi idan ana so muyi wa ƙasa hidima yadda ya dace. Dangane da Kundin Tsarin Mulki ta ƙasa kowacce sashe (na gwamnati) na iyakokinta amma hakan ba yana nufin cewa Gwamnatin Tarayya zata naɗe hannunta ta zura idanu akan abubuwan da suke faruwa a jihohi da ƙananan hukumomi ba. Musamman a harkokin Asusun Haɗingwiwa na Ƙananan Hukumomi. A yayinda cewa Gwamnatin Tarayya ba zata iya bin diddigin duk wasu harkokinsu ba zata tabbatar da cewa an bincika duk wata harka na cin hanci da rashawa a matakai na ƙananan hukumomi. Dangane da duk wata iko da Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa ta bani zanyi ƙoƙari in tabbatar da cewa zan samar da gwamnati mai alhaki da ajiye lissafi a kowacce matsaki na gwamnatin ƙasar nan. Saboda bazan zamo mai gaskiya ba ga 'yan Najeriya idan zan bari wasu su ɓarnatar da dukiyoyinsu a ƙarƙashin kulawa ta.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 23 August 2022.
  • Ko ya ya, duk yadda gwamnatin tarayyar ƙasa ta kai ta fuskar tsari, ba za su iyya cimma nasarorinsu ba sai da tallafi, fahimta da kuma haɗin kai daga kungiyoyin ƙwadago, ƙungiyoyi masu zaman kansu, 'yan jaridu da kuma ma'aikatan gwamnati. Ina roƙan masu ɗaukan aiki da kuma ma'aikata da su haɗe kawunansu wajen bunƙasa samarwa, ta yadda kowa zai ƙaru daga arziki mai bunƙasa. Gidan jaridun Najeriya sun kasance mafi kwarjini a Afirka. Ina kira ga kafafen yaɗa labarai a yau - harda kafafen sadarwa na yanar gizo - da su nuna jarumtarsu ta hanyar kiyayewa da kishin ƙasa.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 24 August 2022.
  • Wannan kira da nikeyi akan haɗin kai sun samo tushe ne daga muhimmancin nasarar da muka samu. Tare da ruguzazzar asusun ƙasa, faɗuwar farashin man-fetur, rashin sirri da basussuka, tattalin arzikin Najeriya na cikin babbar matsala kuma tana buƙatar kulawa na musamman don farfaɗo da ita da kuma shawo kan matsalolin da suka gabatomu, kamar su; Boko Haram, matsalolin Neja Delta, ƙarancin wutar lantarki da kuma rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa. Ya kamata mu bunƙasa sashin ilimin saboda nasarori na tsawon lokaci, Ya kamata lura saosai da fannin kiwon lafiya, ya kamata mu inganta yanayin lalatattun gine-ginenmu.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 24 August 2022.
  • Matsala na kusa-kusan nan itace rikicin Boko Haram. Sojojinmu sun samu nasara acikin 'yan makonnin nan, amma duk da haka cikakkiyar nasara ba zata samu ba idan za'a a bar Iko da Cibiyar bada umurni a Abuja ba. Cibiyar zata koma Maiduguri kuma zata kasance a can har sai an kawo ƙarshen Boko Haram gaba daya. Amma ba zamu iya iƙirarin cin galabar Boko Haram ba har sai mun ceto 'yan matan Chibok da duk wani wanda bai ji ba bai gani ba da ke hannun 'yan ta'addan.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 24 August 2022.
  • Wannan gwamnatin zatayi duk abin da zatayi wajen cetosu a raye. Boko Haram muhimmiyar misali ce ta 'yar ƙanƙanuwar wuta mai jawo katafariyar wuta. Wani irin mai da'awa tare da tsirarun mabiya wanda 'yan sanda suka kashe ba tare da wani haƙƙi na shari'a ba sun sa ya zamo wani fitaccen shahidi. Tun daga wannan lokacin ta hanyar rashin iya aiki na gwamnati, sake, masu kukan cewa ba'a kyautata masu ba sun zamo wata runduna abin tsoro tare da daukan rayukan dubunnan mutane da kuma kame birane da ƙauyuka da dama da ke ƙarƙashin ikon Najeriya.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 24 August 2022.
  • Ƙungiyar Boko Haram ƙungiya ce mara tausayi balle tsoron Allah wanda al'amuransu sun kaucewa koyarwa na addinin musulunci ga duk mai tunani. A ƙarshen wannan rikici idan an kawo ƙarshensu, gwamnati zata ƙaddamar da bincike akan asalin tushensu, abubuwan da suka jawo kafa ƙungiyar, masu tallafa mata, sauran ƙasashen duniya da ke da alaka da ita don tabbatar da cewa an kaucewa sake faruwar ire-iren waɗannan munanan lamuran. A yanzu dai za'a baiwa sojoji cikakken ikon yaƙar ƙungiyar Boko Haram. Zamu tabbatar da tsaida dokokin kai hare-hare don kaucewa tauye haƙƙoƙin ɗan-Adam a yayin da muke kai farmaki. Zamu inganta ayyuka da tsare-tsare na shari'a don tabbatar da cewa an bi duk wata hanya da ta dace wajen kaucewa tauye haƙƙoƙin ɗan-Adam daga sojojin Najeriya.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 27 August 2022.
  • Boko Haram ba ita kaɗai bace matsalar tsaro da ke damun ƙasarmu ba. Akwai miyagun ayyuka kamar garkuwa da mutane, fashi da makami, rikicin Fulani da manoma, satar shanu duka sun haɗe wajen samar da gagarumin rashin tsaro a ƙasarmu. Zamu tabbata. un raini mutane tsayayyu kuma horarru - amintattu - jami'an tsaro masu isashhen al'abashi a tsakanin da kuma - kowanne sashi na tsaro.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 27 August 2022.
  • Shirin yarjejeniyar Neja Delta ya soma ƙarewa a ƙarshen watan Disamba, amma gwamnatinmu tana da niyyar sake sanya hannu sosai acikin wannan aiki da shirye-shiryensu da ake gudanarwa a yanzu. Ina kira ga jagororin waɗannan yankuna da su haɗa kai da gwamnatin tarayya da ta jiha ga waɗannan shirye-shirye na gyare-gyare wanda za'a ƙara inganta su kuma a ƙara musu tasiri. Kamar kullun, a shirye ni ke da in saurari koke-koken sauran 'yan uwana 'yan Najeriya. Na miƙo musu hannuna don abota wajen samar da zaman lafiya da kuma cigaban al'ummar mu.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 27 August 2022.
  • Babu wata sila guda ɗaya da za'a danganta da koma bayan tattalin arzikin ƙasarmu face illolin yanayin jagoranci. Abun kunya ne ga ƙasa da ke da mutumm miliyan 180 ace tana samar da 4,000MW kacal kuma tana rarraba ƙasa da hakan. Cigaba wajen tsantsanin tunani na inganta wutar lantarki da kuma rarraba wutar sun kai ga kashe kudi kimanin biliyan 20 na dalar Amurka tun a shekarun 1999 basu kawo komai ba face duhu, baƙin ciki, ƙunci da asara a tsakanin 'yan Najeriya. Ba zamu bar hakan ya ci gaba ba. Akwai bincike na musamman a yayin wannan canjin mulki wajen gano hanya mafi sauri, lafiyayye akan kuma farashi mai sauƙi wajen kawo wutar lantarki da kuma hutar da 'yan Najeriya.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 27 August 2022.
  • Rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasa na daya daga cikin muhimman ƙudirorin jam'iyyarmu. Zamu shawo kan matsalar nan gaba da gaba ta hanyar farfaɗo da fannin noma, haƙar ma'adanai da kuma bayar da bashi ga masu ƙananun sana'oin hannu don su fara - kasuwancinsu. Zamu binciko hanya mafi sauƙi na farfaɗo da masana'antu da kuma gaggawar gyara da kuma haɓaka titunan jirgin ƙasa, titunan mota da kuma sauran ababen more rayuwa.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 28 August 2022.
  • 'Yan uwana masu daraja, 'yan uwana'yan Najeirya. Ba zan iya tuna lokacin da 'yan Najeriya suka sami fata na alheri daga ƙasashen waje irin na yau ba. Wasiƙu da na amsa daga Gabas da Yamma, daga manyan ƙasashen duniya da ƙanana alamu ne dake nuna cewa ƙasashen duniya sun sanya rai sosai a kanmu. Najeriya ta dalilin haka na da damar cike damammakin da suka cancance ta na tsawon lokaci na ɗago junanmu baki ɗaya da kuma tabbatar da ƙudirinmu na zama shahararriyar ƙasa.
    • "President Buhari's inaugural speech on May 29, 2015". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 29 May 2019. Retrieved 28 August 2022.
  • Mutane idan ma basu yarda da Allah ba ai yunwar cikin su ta gaya masu.

Mahaɗa[edit | edit source]