Wq/ha/Muhammad (SAW)

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Muhammad (SAW)
Allah mai kyau ne kuma yana son mai kyautatawa.

Muhammad dan Abdullahi (Larabci: مُحَمَّد‎, pronounced [muħammad]; c. 570 CE – 8 June 632 CE) ya kasance balarabe, manzo kuma malami, wanda ta shi ne aka samo addinin musulunci. Dangane da koyarwar addinin musulunci, Ya zo don ya jaddada addinin annabawa - Adam, Ibrahim, Musa, Isa (A.S).

Azanci[edit | edit source]

Huɗubar Bankwana[edit | edit source]

Wasu daga cikin sassan su:

  • “Ya ku mutane, tabbas jinin ku, dukiyoyin ku da mutuncin ku daraja ne da martaba a gare ku har sai kun bayyana a gaban ubangijin ku, kamar martabar darajar rana ta yau, da wannan watan naku na yau, da kuma wannan gari mai alfarma (na ku). Tabbas kwanan nan zaku riska ubangijin ku kuma zai tambaye ku akan ayyukan sa kuka yi.”
  • “Ya ku mutane, tabbas gaskiya ne kuna da hakkoki da dama daga wurin matan ku, amma su ma suna da hakkoki akan ku. Idan sun biya hakkokin ku to a gare su akwai hakkin ciyarwa da tufatar wa cikin mutuntaka. Ku kula da matanku yadda ya dace kuma kyautata musu saboda su a gare ku sun kasance abokan zama kuma mataimaka makura”.
  • “Dukkanin ‘yan-Adam sun fito ne daga Adam da Hauwa’u, Balarabe ba shi da fifiko akan wanda ba balarabe ba, haka zalika, wanda ba Balarabe ba bashi da fifiko akan Balarabe, hakazalika, farar fata bashi da fifiko akan bakar fata, face dangane da tsoron Allah da aiki mai kyau. Ku sani cewa duk wani musulmi dan uwan musulmi ne. Ku tuna cewa wata rana zaku bayyana a gaban ubangiji kuma zaku amsa tambayoyi akan ayyukan da kuka yi. Saboda haka ku lura, kada ku karkace daga hanyar gaskiya bayan na tafi”.
  • Duk wanda ya saurare ni to ya mika sako na ga wasu, su ma su mika zuwa ga wasu; sannan kuma ya zamana wanda suka ji karshe su fahimta fiye da wanda suka saurare ni kai tsaye.”
  • Ka zama shaida na yaa Allah, na isar da sakon Ka zuwa ga bayin ka.”
  • “Mafi alkairinku shine wanda ya fi kyautatawa iyalensa, kuma ni ne mafi alkhairin kyautatawa iyali na”.