Wq/ha/Mona Charen
Appearance
Mona Charen Parker (an haife ta Fabrairu 25 ga wata, shekara ta 1957), editar mujallu ce ‘yar Amurka, masabiyar fassarar manufofin siyasa, kuma ..marubuciya. Ra’ayin ta na siyasa shine ra’ayoyin mazan jiya. Charen ta kan yi rubutu akan dokokin kasashen waje, ta’addanci, siyasa, talauci, tsarin iyali, halayyar al’umma, da kuma al’ada. Tayi fice da ra’ayinta na goyon bayan Izra’ila.
Zantuka
[edit | edit source]- Na yi tir da yadda wasu mutane daga ɓangaren mu suka zama munafukai akan masu fyade da masu cin zarafin mata, wadanda ke jam’iyyar mu, wadanda ke zaune a White House, wadanda ke alfaharu harkokin rayuwarsu a wajen aure, wadanda ke alfahari da muzgunawa mata - sannan kuma don kawai yana da kalmar “R” a cikin sunan shi sai muka kawar da kawunanmu… Wannan jam’iyya ce da ta amince da Roy Moore a matsayin sanata a Jihar Alabama, duk da cewa an san shi mai cutar da yara ne. Ba ka iya cewa kana goyon bayan mata kuma ka amince da hakan… Idan ana maganan mutanen banza, akwai wanda ke kan wannan dandali kwanan da ya wuce. Sunan ta Marion Maréchal. To yanzu me yasa tazo nan? Me yasa ta zo nan? Ta kasance yarinya, wacce bata a kujerar siyasa a yanzu daga Faransa. Na san abunda yasa kawai take nan shine saboda sunanta akwai Le Pen. Kuma sunan Le Pen abun kunya ne. Kakanta (Jean-Marie Le Pen) ya kasance mai wariyar launin fata kuma Nazi. Tana ikirarin cewa ta tsaya mai. Amma maganan gaskiya gayyatar da CPAC ta mata abun kunya ne.
- Kamar yadda aka ɗauko daga cikin "Trump’s Takeover of Conservatism Is Complete and Total" (25 ga
watan Fabrairu, shekara ta 2018), by Tim Alberta, Politico