Mira Bai ana kuma rubuta ta da Meera Bai (shekara ta 1498 zuwa shekarar 1547), sufi ce mawakiya ‘yar Indiya kuma mabiyar Krishna. Ta kasance daga cikin sufaye masu tasiri na kungiyar Vaishnava bhakti.