Wq/ha/Medea Benjamin
Appearance
Medea Benjamin (an haifi Susan Benjamin; September 10,a shekara ta 1952), ta kasance mai fafutukar siyasa ce ‘yar Amurka wacce ta taimaka wajen ƙirƙirar w:Code Pink da kuma kungiyar dillanci na adalci Global Exchange.
Zantuka
[edit | edit source]- Bari mu ɗauka al’amari daya kawai, kuma akan dakarun sojojin Amurka a kasashen waje, akwai akalla fiye da sansanin sojojin Amurka 800 a ƙasashen waje. Mafi akasarinsu basu da wani takamaiman amfani na tsaron ƙasa. Sun kasance wani abu na Yakin Duniya na II. Mai yasa muke bukatar sansanin sojoji a Jamus, a Italiya? Muna da su a Korea yanzu, alhali akwai tattaunawa na zaman lafiya da Korea, amma har wayau muna da dumbin sansanin soja a Korea. A hakikanin gaskiya fiye da guda 80.
- Interview "The Green New Deal Must Fight Militarism, by Dharna Noor, The Real News Network (17 December 2018)