Jump to content

Wq/ha/Mary Cassatt

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Mary Cassatt
portrait of Mary Cassatt, by Edgar Degas, c. 1880-84


Mary Cassatt (Mayu 22 ga wata, shekara ta 1844 Yuni 14 ga wata, shekara ta 1926), mai zane ce ‘yar Amurka kuma mai buga da zane. An haife ta a Pennsylvania, amma ta kwashe tsawon rayuwarta na zane a Faransa, inda ta fara abota da Edgar Degas, kuma daga bisani tayi baje koli tare da impressionists. Cassatt ta kan yi zanen hotunan rayuwar gida da kuma zamantakewa na mata, tare da mayar da hankalin akan tsananin shakuwa tsakanin uwaye da ‘ya’ya.

Zantuka

[edit | edit source]
sorted chronologically, by date of the quotes of Mary Cassatt
Mary Cassatt, 1875: 'Tsintar fure a fili, zanen-mai a sarari; inda zane yake a yanzu: National Gallery of Art, Washington D.C.
Mary Cassatt, 1878: 'In the loge', oil-painting on canvas; current location: Museum of Fine Arts, Boston
Mary Cassatt, 1880: 'Uwa zata yi wa dan ta mai jin bacci wanka’, zanen mai a canvas; inda zane yake a yanzu: Los Angeles County Museum of Art, U.S.
  • Oh wani iri nake ji in fara aiki, yatsu na suna kaikayi sosai kuma ruwan idanu na sun kosa su sake ganin hoto mai kyau.
  • Na hakura da dakin hoto kuma na yaga hoton mahaifina, kuma ban taɓa burushi ba tsawon makonni shida, ba kuwa zan taba karawa ba har sai na ga alamun komawa Turai. Na kosa matuka in koma Turai damina mai zuwa sannan in samu aiki, amma ban yanke shawarar a ina ba.
    • An ɗauko daga wasikar ta na watan Yuli, shekara ta 1871; kamar yadda aka dauko daga tarihin rayuwarta a yanar gizo a [1].
  • …Mu ‘yan [ Impressionist ] zamu dauki fada mara alamun nasara kuma muna bukatar duk wasu dakarun mu.
  • Idan dai kai [ Vollard ] zaka iya nemo wannan hoton [‘Milliners's workshop'] wanda Edgar Degas ya zana, na san dan Amurka wanda zai biya komai saboda da shi.
    • Mary Cassatt, quoted by Paris' art-dealer [Vollard] , in Degas, an Intimate Portrait, Courier Corporation,a shekarar 1927, p. 90