Jump to content

Wq/ha/Martin Luther King Jr.

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Martin Luther King Jr.
Dole ne mu gano ƙarfin soyayya, karfi, da ƙarfin fansar soyayya. Sannan a lokacin da muka gano hakan zamu iya mayar da wannan tsohuwar duniyar sabuwa. Zamu iya mayar da mazaje nagari. Ta hanyar soyayya kawai.

Dr. Martin Luther King Jr.(15 ga watan Janairun shekarar 1929 zuwa 4 ga watan Afrilun shekarar 1968) ya kasance Ministan Baptiza dan America, mai fafutukar ‘yancin ‘yan ƙasa, kuma wanda ya lashe lambar yabo na Zaman Lafiya wato Nobel Peace Prize a shekarar 1964.

Zantuka

[edit | edit source]
Zaman lafiya na ainihi ba wai rashin tashin hankali bane: shi wanzuwar adalci be.

Shekara ta 1950s

[edit | edit source]
  • Mu, wadanda bamu da gado a wannan kasa, mu wadanda ake muzguna ma wa na tsawon lokaci, mun gaji da wanzuwa cikin darare masu tsawo a tsare. Sannan yanzu, muna masu riska zuwa hasken yini na ‘yanci, adalci da kuma rashin nuna bambanci.
    • Jawabi a Montgomery Bus Boycott, a Cocin Baptiza na Unguwar Holt Street (5 ga watan Disamba, shekara ta 1955).
  • Muna nan, mun fito nan a cikin wannan maraice saboda mun gaji yanzu. Kuma ina so in fada cewa ba mun zo nan don mu tada husuma bane. Bamu taba yin hakan ba. Ina so ya zama sananne a gabaki ɗaya yankin Montgomery da kuma daukakin kasar nan, cewa mu Kiristoci ne. Munyi imani da addinin Kiristanci. Munyi imana da koyarwar Yesu. Makami kadai da muke dauke da shi a cikin wannan yinin shine makamin zanga-zanga. Shi kenan.
    • Jawabi a Montgomery Bus Boycott, a Cocin Baptiza na Unguwar Holt Street (5 ga

watan Disamba, shekara ta 1955).

  • Ba mu kan rashin dai-daito, bamu akan rashin daidai a cikin abunda muke yi. Idan muna kan rashin daidai to Kotun Koli na ƙasar nan ba ya kan daidai. Idan bamu kan dai-dai, to Kundin Mulkin ƙasar Amurka ba a kan daidai yake ba. Sannan kuma idan bamu kan dai-dai to Ubangiji Madaukaki ba ya kan daidai. Idan bamu kan daidai, to Yesu Almasihu ya kasan mafarki ne kawai bai taba sauko wa zuwa ga duniya ba. Idan bamu kan daidai, to doka karya ce, soyayya ba ta da wata ma’ana. Sannan mun ƙudurin aniya a nan Montgomery zamuyi aiki kuma zamu fafata, “har sai adalci ya kwarara a kasa kamar ruwa, kuma daidaito ya wanzu kamar makeken kogi”.