Wq/ha/Maria Rosa Antognazza
Appearance
Maria Rosa Antognazza (1964 '4– 28 ga watan Maris, shekara ta 2023), ta kasance masaniyar falfasa 'yar Burtaniya kuma Farfesan Falsafa a makarantar King's College.
Zantuka
[edit | edit source]- Ina kaunar damar yin tunani akan manya-manyan tambayoyi da falsafa ke tambaya, da kuma hanyoyi na musamman da falsafa ke horar da zuciya wajen amsa wadannan tambayoyi. Menene yake gaskiya? Me yasa yake akwai wani abu maimakon babu komai? Shin akwai wata halitta ta musamman ko kuwa halittu ne da dama? Menene ilimi kuma menene muke iya sani? Shin akwai wani abu wanda yake musunta shi daidai ko kuskure? Ko kuwa komai yana da alaka? Mutane da dama a wasu lokuta za'a fuskance su da wadannan tambayoyi, kuma zasu yi kokarin amsa su a cikin salo na ilimi ko akasin haka. Falsafanci ya kasance yana tauye su tsawon karni da dama a cikin salo na ilimi, rikitattun salo, yana shigar da su a cikin wani yanayi mai zurfi, mai cike da mamaki, da tattaunawa masu kayatarwa wanda ake yi har zamanin yau.
- A kan tambaya "When and what was responsible for you becoming interested in your academic discipline?", at kcl.ac.uk, a shekarar 2015.
Hanyoyin hadin waje
[edit | edit source]- Professor Maria Rosa Antognazza, King's College London