Wq/ha/Mamman Shata

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Mamman Shata

Alhaji Mamman Shata wani shahararren mawakin gargajiya ne na Hausa wanda yayi fice a kasashen Hausa da nahiyar Afirka, kai harma da duniya baki daya.

Kalaman Hikima[edit | edit source]

  • Allah ya yarda, har yau ni ke yi, ba'a samo canji na ba, balle wai in zauna har wai ince huta in dan sirara; wani huta Shata, ka rika dai..
  • Allah bai taba yin zambo ba, Ni kuma bana zagin kowa..
  • Amma fa uwata in za’a yi mani aure, Goggo idan za’a yi man aure, Inna idan za’a yi mani aure, Baba idan za’a yi man aure, KAwu idan za’a yi man aure, A bar ni in zabi fari kyakykyawa, Kar da a bani baqi mummuna, Auren tilas ba aure ne ba, Shi kesa wasu yawon banza
  • Kowa ka gani na sabon Allah
  • ko wanene ke kafirci, kun san, babu kamar Fir'auna.
  • Kai mutane kowa yake addini, kun san baya kamar manzon Allah.
  • kowa ya san kowa Katsinawan Dikko, ku da Kanawan Dabo, da mutanen Zazzau. Hada da Jasawa namu, Filanin Yola. Shata tafi Gwambe kai ne, balle Bauchin Yakubu, Mamman shiga Barno ni ne..
  • Don ba'a gwaninta da tsoro Malam, mai tsoro bashi gwaninta ko wanene, kuma ko dan wa..
  • Matsoraci bashi zama gwani ko wanene.. ka zama kamar ni filin waka, sararin waka ban tsoro, in na fito, Shata ne- kun san shi, ya san ku, sai kaka?
  • Gurnanin Damisa karen gida ke gudu, karen ko na wanene dan kusun uwa

Manazarta[edit | edit source]

  1. LHX, TRANSSION:. "Bakandamiyar Shata - Mamman Shata MP3 download | Bakandamiyar Shata - Mamman Shata Lyrics | Boomplay Music". Boomplay Music - WebPlayer. Retrieved 19 August 2022.
  2. "Mamman Shata". Lyricsahel. Retrieved 19 August 2022.
  3. www.gumel.comhttp://www.gumel.com/hausa/littattafai/kabiru-fagge/shata/bakandamiya.htm. Retrieved 19 August2022.