Malebogo Molefhe (An haife ta a shekarar 1980) ‘yar wasan kwallon kwando ce ‘yar Motswana wacce ta zama mai fafutukar haƙƙin a kan zalunci na wariyar jinsi bayan an harbe ta sau takwas. A cikin shekara ta 2017, ta samu Lambar Yabo ta Mata na Ƙasa da Ƙasa a kan Jarumta.
Samun damar buɗe zuciya yana koyar da dabi’u na musamman da dama a kan kanka ya kuma kara maka dogaro da kai wajen kallon duniya baki ɗaya, ka rika fuskantar su kuma kana karawa kan ka karfin gwiwa.
Yana da muhimmanci sosai mata su gane cewa akwai manyan iko da za su iya riska ba tare da sun dogara da maza ba.
Babban kaskancinmu mu mata shine, rashin kai rahoton matsaloli ko kuma janye su a yayin da ya kamata mu bari doka ta yi aiki, wannan kaɗai ya ci karo da tsarin yakin mu a kan daidaiton jinsi.