Wq/ha/Maitama Sule

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Maitama Sule
Maitama Sule

Yusuf Maitama Sule (1 ga watan Octoban 1929 zuwa 3 July 2017) ya kasance ɗan siyasa ne a Najeriya, jami'in diplomassiyya wanda ake yiwa laƙabi da sarautar Ɗan Masanin Kano.

Kalaman Hikima[edit | edit source]

  • Ina tunanin cewa muna buƙatan muyi wa gwamnati addu'a kuma muna buƙatan mu ƙara haƙuri. Ya kamata mu samu tsari mai kyau. Najeriya babbar ƙasa ce, kuma tana da ikon jagorancin tattalin arziƙin Afurka.
    • NTA News, Nigeria's former representative to United Nations Dr. Maitama Sule speaks on current fuel crisis. !2th April 2016. Retrieved 1st September 2022.
  • Ya shugaban kasa: ina ganin Najeriya a ƙarƙashin mulkinka zata zamo abin da ake tsammaninta dashi; saboda nayi mafarki cewa Najeriya wata rana zata zamo ƙasa guda; nayi mafarki cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa, nayi mafarki cewa Najeriya zata samar da wani sarari na siyasa da za ta jagoranci Nahiyyar Afurka da duk wani baƙin fata a duniya; nayi mafarki cewa Najeriya zata zauna a matsayin da ya dace da ita a fuskar sauran ƙasashen duniya, sannan waɗannan mafarke-mafarken za su zamo gaskiya ne a ƙarƙashin mulkin ka ya shugaban kasa..
    • NTA News, Nigeria's former Permanent Rep. to UN. Yusuf Maitama Sule Raises Hope on Nigeria. 13 September, 2015. Retrieved 1st September 2022.
  • Nayi mafarki ba ga Arewacin Najeriya ba kaɗai amma ga ɗaukakin ƙasar Najeriya. Nayi mafarki cewa wata rana Najeriya zata zamo ƙasa guda (mai haɗin kai) da gaske. Nayi mafarki cewa Najeriya za ta samu tattalin arziƙi mai karfi. Na yi mafarki cewa, Najeriya zata samar da wani sarari na siyasa da za ta jagoranci Nahiyyar Afurka da duk wani baƙin fata a duniya. Nayi mafarki cewa 'yan Najeriya zasu zamo masu zumunci da kare hakkokin 'yan uwansu 'yan Najeriya. Na yi mafarki cewa Najeriya zata zauna a matsayin da ya dace da ita a fuskar sauran ƙasashen duniya kuma za ta zamo ƙasa na kan gaba a duniya. Idan Allah ya yarda. Kuma dukanin munanan abubuwan da ke faruwa zasu zo ƙarshe idan Allah ya so ya yarda.
    • Channels Television, Northern Leaders Congress: Maitama Sule Asks Nigerians to Unite. 10th March 2014. Retrieved 2 September 2022.
  • Allah ne kaɗai bai da farko kuma bai da ƙarshe. Duk abinda ka ke gani, mai kyau ko mara kyau yana da farko kuma yana da ƙarshe. Kuma idan Allah ya yarda zamu ga ƙarshen zalunci a Najeriya. Da izinin Allah zamu zo mu san zaman lafiya da kwanciyan hakali a Najeriya. Kuma idan Allah ya yarda zamu zamo masu kula da haƙƙoƙin 'yan uwanmu 'yan Najeriya. Amma abun baƙin ciki shi ne ba abin da ke faruwa ba kenan a yau, kuma hakan yasa nike nuna damuwa ta kuma ni ke aiki akan gyara hakan.
    • Channels Television, Northern Leaders Congress: Maitama Sule Asks Nigerians to Unite. 10th March 2014. Retrieved 2 September 2022.
  • A yau, Najeriya ba ta kasance ƙasar da ta ke ba a da, Najeriya ta kasance ƙasa mai mutunci, mai dauke da mutane masu kyawawan halaye, amma a yau, ko ma'aikatun jama'a na gurɓacewa a yau, ladabi ga magabata kaman ni da kuma dokokin ƙasa sun kasance tushen kyawawan halaye ga mutanenmu amma a yanzu duk sunyi rauni. Gaskiya a inda baza a samu riba ba ya zamo wani sabon abu na daban. Tausasawa juna da makamantansu. A taƙaice dai, babu sauran muhimmanci ga falfasa, rashin tsaro a siyasa, tashe-tashen hankali a siyasa, rashin ɗabi'u na gari ga mutanenmu, cin hanci da rashawa a tattalin arzikinmu, rashin cigaba a kimiyya da kuma rashin fasahar ƙere-ƙere.
    • Channels Television, Northern Leaders Congress: Maitama Sule Asks Nigerians to Unite. 10th March 2014. Retrieved 2 September 2022.
  • Da gaskiya da adalci ne kadai za'a iya rike mulkin Najeriya
    • Maitama Sule and Northern Leaders Forum visit Buhari, 12 May 2015. Retrieved 3rd September 2022.
  • Dole ayi adalci ga duk wanda ya dace
    • Maitama Sule and Northern Leaders Forum visit Buhari, 12 May 2015. Retrieved 3rd September 2022.
  • Za'a iya barin iko a hannun kafiri idan har zai yi adalci, amma baza'a bar iko a hannun musulmi ba matuƙar ya kasance bashi da tausayi da kuma adalci.
    • Maitama Sule and Northern Leaders Forum visit Buhari, 12 May 2015. Retrieved 3rd September 2022.
  • Duk inda ka ga ana rikici a ko ina a faɗin duniya to tabbas an tafka rashin adalci ne. Maslaha ga wannan rashin adalci kuwa shine adalci
    • Maitama Sule and Northern Leaders Forum visit Buhari, 12 May 2015. Retrieved 3rd September 2022.
  • Duniyar ita kanta ba za'a iya mulkar ta da tilastawa ba kuma ba da tsoro ba ko kuma don ƙarfin iko.

Manazarta[edit | edit source]