Wq/ha/Mahatma Gandhi
Appearance
Mohandas Karamchand Gandhi (2 ga watan Oktoban shekarar 1869 zuwa 30 ga watan Janairun shekarar 1948) lauya ne dan ƙasar Indiya, mai kishin kasa mai adawa da mulkin mallakan turawa, kuma ɗan siyasa wanda ya jagoranci gwagwarmayar neman ‘yancin kasar Indiya daga hannun turawan Burtaniya.
Zantuka
[edit | edit source]Shekara ta 1890’s
[edit | edit source]Indiyawa ba zasu yi nadamar damar ‘yan kasa da suyi amfani da sunan ƙasar su. Zasu yi nadama ne idan akasin hakan ya faru. Sun tabbatar da cewa, su ma da kansu, idan dama ta samu su samu hakkin. Ku kuwa a cikin hikimar ku ba zaku bar ‘yan Indiya ko kuma ‘yan asalin kasa su samu wadannan kyawawan hakkoki na musamman ba, saboda suna da fata mai duhu.
- Times of Natal, Oktoba 26 ga wata, shekara ta 1894, in Collected Works of Mahatma Gandhi, vol. 1, pp. 166-67.
- Namu shine cigaba da gwagwarmaya akan wani nau’in ƙasƙantarwa da Turawa ke ƙoƙarin ƙaƙaba mana don mu zamo tamkar mutanen Kaffir wanda aikinsu kawai farauta ne, kuma muhimmin burinsu shine su tara shanu don su siya mata dasu, sannan su hayayyafa a cikin shagala da tsiraici.
- Address given in Bombay (26 ga watan Satumba, shekara ta 1896), Collected Works of Mahatma Gandhi, Vol. 1, p. 410 (Electronic Book), New Delhi, Publications Division Government of India, 1999, 98 volumes.