Jump to content

Wq/ha/Lila Downs

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Lila Downs
Lila Downs a shekara ta 1801


Ana Lila Downs Sánchez (an haife ta 9 Satumban 1968), mawakiya ce ‘yar Mexico kuma ‘yar wasan kwaikwayo.

Zantuka[edit | edit source]

  • Har yanzu iyakar ba ta da ma’ana a zuciya na. Wuri ne da ke da dumbin abubuwa da ke faruwa, dumbin labarai marasa dadi, dumbin labarai masu dadi, mutane da dama wadanda ke neman karya dokoki kuma su bayyana abubuwa da dama da hakan. Ina jin dadin karya dokokin.
    • A kan yadda iyakar Amurka da Mecico ke tasiri ga aikin ta a cikin “Mex factor” in The Guardian (2003 Feb 10)
  • Inaga yana da kyau mu tuna wa kawunanmu cewa dukkanmu baki ne a da, kuma mu rika jinjinawa mutanen da ke sanya lemu a cikin ruwan ‘ya’yan itace na lemu da kuma masu sanya strawberry a cikin cake din mu.
    • A cikin hirar ta akan Woody Guthrie’s “This Land is Your Land” a cikin jerin wakoki don bayyana abubuwan da ‘yan gudun hijira ke fuskanta a cikin “Mex factor” a cikin the Guardian (2003 Feb 10)
  • Ina tsammani na yi tasiri a kan dumbin zamanin ‘yan wasa na Mexico. Ina alfahari da hakan saboda ba abu bane mai sauki a wannan fage. Amma kuma haka zalika yana da sauki saboda abu ne da kake jin dadin yi, kuma abu ne da kake sha’awa. Har a lokacin ka na rauni wakokin ka na tattare da kai.