Wq/ha/Leo Tolstoy
Lev Nikolayevitch Tolstoy Никола́евич Толсто́й, akan kira shi da Leo Tolstoy, ko wasu lokutan Tolstoi] (9 September 1828 – 20 November 1910), ya kasance marubuci dan kasar Rasha, masanin falsafa, dan siyasan zamantakewa, wanda littattafansa guda War and Peace da kuma Anna Karenina ake daukansu a matsayin muhimman littattafai a duniya.
Zance[edit | edit source]
- Jarumin labari na, wanda nike so da duk wani karfi na ruhi na, wanda nike kokarin kwaikwayonsa a kowanne kyawunsa, wanda ya kasance, shine, kuma zai zama mai kyau, shine Gaskiya.
- Sevastopol in May (1855), Ch. 16
- Kafa hudu na fili shi ne kadai abunda yake bukata
- Mutum yana iya rayuwa ba tare da ya kashe dabba ba saboda abinci; saboda haka, idan ya ci nama, ya taka rawa a wajen kashe dabba kawai saboda kwadayinsa. Kuma ya yi aiki ta rashin da'a
- Writings on Civil Disobedience and Nonviolence (1886)
- Na zauna a bayan mutum, na shake shi, kuma ina sa shi yana dauka ta, kuma a hakan ina tabbatar wa kai na da kuma sauran jama'a cewa ina matukar tausaya masa kuma ina so in rage wahalarsa ta kowacce hanya, face sauka daga bayansa.
- Writings on Civil Disobedience and Nonviolence (1886)
- Farin cikin rayuwar maza na kunshe a cikin rayuwa. Sannan rayuwa na kunshe da aiki.
- What Is To Be Done? (1886) Chap. XXXVIII, kamar yadda aka fassara daga The Novels and Other Works of Lyof N. Tolstoï (1902) Nathan Haskell Dole ya gyara, p. 259