Jump to content

Wq/ha/Käthe Kollwitz

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Käthe Kollwitz
Gaskiya mai sauki akan zancen shine ina mai samun kananan aiki abu mai kyau

Käthe Schmidt Kollwitz (July 8, 1867 – Afurelu 22, 1945) ta kasance mai zane ‘yar Jamus, mai kirkirar zane, kuma mai sassaka wanda ayyukanta suka nuna kayatattun halin rayuwa a farkon rabin karni na 20. Tana nuna tausayinta ga masu karamin karfi ta hanyar zanen ta, sassake-sassaken ta don tausayawa wanda talauci, yunwa da kuma yaki ya shafa.

Zantuka[edit | edit source]

Na fara fuskantar wani lokaci na gama gari a rayuwata inda aikk shine farko.
Na ji cewa ban da wani iko na janye matsayi na a matsayin mai fafutukar ‘yanci. Hakki na ne da inyi magana akan wahalhalun da mutane ke sha, wahalhalu da basu taba karewa kuma suna da girma kaman tsaunuka.
Fafutukar ‘yanci (Pacifism) ba wai kawai batun nuna natsuwa bace, batun aiki tukuru ce.
Trans. Richard and Clara Winston, ed. Hans Kollwitz, Regnery Pub.; republished by Northwestern University Press, 1988
  • Na fara fuskantar wani lokaci na gama gari a rayuwata inda aikk shine farko. A yayin da duka ‘ya’ya na suka yi tafiya don hutun Ista, yana da wuya inyi wani abu face aiki. Inyi aiki, inyi bacci, in ci abinci sannan in fita ‘yar gajerar tattaki. Amma fiye da komai aiki nake yi. Amma duk da haka nakan yi mamakin ko babu albarka a wannan aikin. Ba tare da an karkatar da hankali na zuwa wani wuri ba, ina aiki kamar yadda shanu ke huda.
    • Diary entry (12 January 1912)
  • Zuwa karshen kashi na uku na rayuwa aiki kawai ya rage. Shine kadai yake tunzurawa, yake maido da kuzari, yake saka farin ciki ya kuma cika buri.
    • Diary entry (12 January 1912)