Wq/ha/Jose Maria Arancibia
José María Arancibia (11 ga watan Afrilu, shekara ta 1937) ɗan asalin Argentine ne na Cocin Katolika wanda ya yi aiki a matsayin babban Bishop na Archdiocese na Mendoza.
Zantuka
[edit | edit source]Amincewa, tattaunawa, da abokantaka a tsakanin 'yan Argentina, musamman ma a cikin yanayi na rikici, yana buƙatar ayyukan jaruntaka daga dukkan 'yan ƙasa. Ya zama wajibi musamman ga wadanda ke da mukaman siyasa da zamantakewa. Bishops na ci gaba da yin kira da a yi addu'a da tattaunawa don fuskantar rikici tsakanin yankunan karkara da gwamnatin kasa: "Ya kamata mu dauki matakai don haduwa da tattaunawa." (16 ga watan Yuni, shekara ta 2008). Gaskiya game da mutum sharadi ne da ya wajaba don samun 'yanci. A cikinsa ne za'a ta ginu, wanda ya qunshi fayyace madaidaicin tsari na rayuwa da mutuwa, ayyuka da haqqoqi, aure, iyali da al'umma, har ma da kula da yanayi. Al'umma mai girma ba zata iya dogaro da akidar karya ba, ko kuma amfanuwa da wasu 'yan kadan, sai dai ta damu da kare raunana. "Dole ne babbar al'umma ta kare masu rauni": Nasiha na Akbishop Mendoza (12 ga watan Yuli, shekara ta 2012).