Jump to content

Wq/ha/Hlubi Mboya Arnold

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Hlubi Mboya Arnold

Hlubi Mboya Arnold,(an haife ta 2 ga watan Maris, shekara ta 1978), ta kasance jarumar, fim ‘yar Afurka ta Kudu, wacce ta taka muhimmiyar rawa a wasan soap opera a matsayin Nandipha Sithole. Ta taka rawa na musamman a cikin shirin telebijin na Afurka ta Kudu mai suna Dora's Peace, inda ta samu lambar yabo ta SAFTA a matsayin jaruma ta biyu.

Zantuka

[edit | edit source]
  • Ni kaina ba tsaftatacciya bace tas, na yi kura-kurai da yawa, amma hakan ne ya sa na zamo macen da nike a yau.
  • Wasu abubuwan basu taba canzawa kuma wadannan abubuwa a wuri na sune ka’idoji da gaskiya da soyayya.
  • Oh Allah na, wasan kwaikwayo hanya ce a gare ni da zan riski zukata kuma in isar da sako akan abunda na yi imani da shi.
  • Akwai abunda ya kamata ya rika damunka a zuciya wanda zai sa ka tashi ka nemi arziki.

Hanyoyin waje

[edit | edit source]

w:Hlubi Mboya