Jump to content

Wq/ha/Halima Atete

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Halima Atete

Halima Yusuf Atete, Ta kasance wacce aka fi sani da Halima Atete (an haife ta a ranar 26 ga watan Nuwamban shekara ta 1988) ƴar wasan fina-finan Najeriya ce kuma mai shirya fina-finai, haifaffiyar jihar Borno kuma ta tashi a Maiduguri, jihar Borno.Ta shiga kannywood ne a shekarar 2012, ta fara fitowa a cikin shirin Asalina (My Origin) wani fim da ta shirya, bayan fitowarta a fina-finai da dama kamar su Kona Gari, Asalina, Dakin Amarya, ta lashe sabuwar jaruma a fim. lambar yabo ta City People Entertainment Awards a shekarar 2013, wata kungiyar labarai ta Africa Voice ta London ta zabe ta a kan kyakkyawan aikinta a masana'antar nishaɗi.

Zantuttuka

[edit | edit source]
  • Dukkanmu muna da makiya amma a kullum sai na tabbata na yi addu’a sosai san nan sai na bar komai a hannun Allah. Ka sani yanzu ko da ba ka da komai a rayuwa, to sai ka samu wanda bai sonka.
  • Kayi haƙuri ka dage a dukkan abubuwan da kasa a gaba.Ba komai bane ake samu da sauƙi,amma idan ka dage ka cigaba da addu'a to insha Allah zaka cimma nasara.
  • Lokacin da na fara shirin fim ɗin Asalina, na samu goyon baya sosai daga masoya da kuma ƴan uwa, wannan ne ya ƙara min ƙwarin guiwa wajen cigaba da shirin fina-finai.