Jump to content

Wq/ha/Fawzia Koofi

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Fawzia Koofi
Fawzia Koofi

Fawzia Koofi (Farasiya: فوزیه کوفی; an haife ta a shekara ta 1975) 'yar siyasar Afghanistan ce kuma mai fafutukar kare hakkin mata. Asali daga lardin Badakhshan take, Koofi ta kasance mamba a kwanan baya a cikin tawagar Afghanistan da ke tattaunawa da Taliban a Doha Qatar. Tsohuwar 'yar majalisa ce a Kabul kuma ta kasance mataimakiyar shugaban majalisar dokokin kasar.

Zantuka

[edit | edit source]
  • Fawzia Koofi
    A cikin wasiƙar da ta rubuta zuwa ga mahaifiyarta, Koofi ta rubuta: “Na koya daga gare ku cewa ilimin karatu kaɗai bai isa yayi renon yara nagari ba, amma hankali, haƙuri… da sadaukarwa. Wannan shi ne misalin matan Afganistan, mata irinku waɗanda za su yi tafiya mai nisa da komai a ciki don tabbatar da cewa yaranku sun isa makaranta.”
  • A ra'ayinta, yin magana da Taliban game da sulhu kuskure ne, "wani gyaran gaggawane na gajeren lokaci wanda ba zai yi wani abu ba don magance matsalolin duniya." Ta shawarci ’ya’yanta mata da kada su ji tsoron wani abu idan har ba za ta koma gida wata rana ba: “Ina rayuwa ne domin ku—’yan mata masu daraja—za ku sami ’yanci ku yi rayuwarku kuma ku yi mafarkin dukan mafarkinku."