Wq/ha/Fatima Akilu
Appearance
Fatima Akilu ƴar Najeriya ce ƙwararriya a ilimin Nazarin halayyar ɗan adam, marubuciya, malama, tsohuwar jami’ar gwamnati, mai bayar da shawara kan ilimi kuma mai magana da yawun jama’a a fagagen hanawa da daƙile tashin hankali (CVE) da kuma yaki da ta’addanci. A halin yanzu ita ce babbar darekta a gidauniyar Neem kuma tsohuwar daraktar nazarin halayyar ɗan Adam da dabarun sadarwa a ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a Najeriya, inda ta taimaka wajen bunƙasa shirin yaƙi da ta'addanci na farko a ƙasar. Fatima Akilu wani bangare ne na kungiyar Global Strategy Network tare da masanin masana'antu Richard Barrett da sauran mutane
Zantuka
[edit | edit source]- A sauƙaƙe sanya mutane a gaba, ba da fifiko ga martani ga waɗanda abin ya shafa kuma tabbatar da cewa an tallafa wa al'ummomi don sake gina rayuwarsu.
- Ra'ayin ta a wata hira
- Mata suna rike da mabuɗin duk wani shiri na samar da zaman lafiya yayin da suke fuskantar rikici ta wata hanya dabam da maza. Sun kasance suna ɗaukar nauyi a matsayin iyaye mata, mata, 'yan'uwa mata, mahalarta da masu ceto, duk da haka har yanzu an cire su daga teburin mafita. Mun gano cewa lokacin da aka haɗa mata cikin yanke shawara za'a fi mayar da hankali ga magance hanyoyin soja. Ina jin cewa mata idan an kira su suna yawan zama a matakin kananan hukumomi amma muna bukatar karin mata a manyan matakan gwamnati musamman bangaren tsaro