Wq/ha/Eleanor Roosevelt

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Eleanor Roosevelt
Yana daukar jarumta wajen soyayya, amma jin raɗaɗi a dalilin soyayya wuta ce mai tsafta wanda wadanda suka yi soyayyar gaskiya ne kawai suka sani.

Eleanor Roosevelt (11 Oktoban 1884 – 7 Nuwamban 1962), ‘yar siyasar zamantakewa ce, matar tsohon shugaban kasar Amurka Franklin Delano Roosevelt.

Zantuka[edit | edit source]

Ka yi abunda kake gani daidai ne a cikin zuciyarka - saboda za’a rika aibanta ka ko yaya. Domin za’a yi, tir da kai ida ka yo, kuma za a yi tir da kai idan baka yi ba.
  • Oh! Ina so in sanya hannuwa na a jikin ki (rungume ki), Ina mararin rike ki kusa da ni. Zobenki matukar nutsuwa ne (a gareni), Na kalle shi nayi tunani, tana so na ko kuwa ba zan taba sanya shi ba.
    • A cikin wani Wasika zuwa ga Lorena Hickok, March 7, 1933
  • Ka yi abunda kake gani daidai ne a cikin zuciyarka - saboda za’a rika aibanta ka ko yaya. Domin za’a yi, tir da kai ida ka yo, kuma za a yi tir da kai idan baka yi ba.
    • Kamar yadda aka dauko daga cikin How to Stop Worrying and Start Living (1944; 1948) daga Dale Carnegie; duk da cewa ana alakanta Rooselvet da ainihin maganan, “ayi tir da kai idan ka yi, ayi tir da kai idan ka bari”. An sanya shi a cikin alamun quotation don nuna cewa itama tana da tasiri akan maganan. Ya samo asali daga shekarar 1836 daga evangelist Lorenzo Dow.
  • Fahimta kamar unguwa ce mai hanya biyu.
    • kamar yadda aka dauko daga Modern Quotations for Ready Reference (1947) by Arthur Richmond, p. 455
  • Bai isa ba kawai ka yi magana akan kwanciyar hankalin ka, dole ne mutum yayi imani da shi. Kuma bai isa ba kawai mutum yayi imani da shi. Dole ne yayi aiki akan shi.
    • Voice of America broadcast (11 November 1951)
  • Dole ne mu fuskanci gaskiya cewa ko dai zamu mutu tare, ko kuma zamu koyi yadda zamuyi rayuwa a tare, sannan indai zamuyi rayuwa tare to dole ne mu tattauna.
    • The New York Times (1960), kamar yadda aka hakayo daga cikin The Beacon Book of Quotations by Women (1992) daga Rosalie Maggio, p. 156