Wq/ha/David Aaronovitch
Appearance
David Morris Aaronovitch (an haife shi 8 ga watan Yuli, shekara ta 1954) dan jaridar kasar Ingila ne, mai gabatar da labarai kuma marubuci. Shine marubucin Paddling to Jerusalem: An Aquatic Tour of Our Small Country (a shekarar 2000),, Voodoo Histories: the role of Conspiracy Theory in Modern History (2009) da kuma Party Animals: My Family and Other Communists (2016). Ya lashe lambar yabo ta Orwell Prize don aikin jaridar siyasa a 2011, da kuma lambar yabo na “marubucin babi” na Abun da takaddu suka ce a shekara ta 2003. Yayi aiki da gidan jaridu irin su The Independent, The Guardian da kima The Times.
Zantuka
[edit | edit source]- [A kan mahaifiyar shi] Ta kasance bata goyon baya idan na bar gashi na yayi tsawo, kuma haka zalika bata goyon bayan cewa bayan wasu ‘yan lokuta na yanke shi. Ina da ra’ayin, a kaina, in bar shi yayi tsawo.
- An ciro daga Party Animals: My Family and Other Communists, London: Jonathan Cape (a shekarar 2016), kamar yadda Rachel Cooke ya hakayo daga cikin "David Aaronovitch: Me, Mum, Dad… and Stalin", The Observer (10 January 2016)