Jump to content

Wq/ha/Bola Ahmad Tinubu

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Bola Ahmad Tinubu

TAKAITACCEN TARIHIN BOLA AHMAD TINUBU.

Bola Ahmad Tinubu
An haifeshi a ranar 29, ga watan Maris,a shekarar 1952 cikin birnin Legas.

Bola Ahamad Tinubu, musulmi ne kuma ya halarci makarantar firamare mai suna St. John's Primary School, da ke Aroloya da ke birnin Legas, sai sakandiren Children's Home School da ke Ibadan.

Tinubu ya samu tafiya kasar Amurka domin karo karatu a shekarar 1975, inda ya fara karatu a kwalejin Richard J. Daley College da ke Chicago, Illinois kafin daga bisani ya koma jami'ar jihar Chicago mai suna Chicago State University.

Ya samu kammala digirin sa a shekarar 1979 daga wannan jami'ar inda ya karanci Ilimin gudanarwar kuɗi wato "Accounting".

Tinubu ya yi aiki da kamfanin Amurka mai suna Arthur Andersen, da kuma wasu kamfanonin irinsu Deloitte, Haskins, & Sells, da GTE Services Corporation duk a can Amurka.

Bayan komowarsa gida Njeriya a cikin shekarar 1983, Bola Tinubu ya soma aiki da kamfanin Mobil Oil Nigeria, kafin daga bisani ya zamo cikin jagororin kamfanin.
Ya fara shiga harkokin siyasa ne a shekarar 1992, lokacin da ya shiga jamiyyar Social Democratic Party (SDP) inda ya zamo mamba na Naijirar  'Peoples Front' wanda marigayi Shehu Musa Yar'Adua ke jagoranta, ɗarikar da ta ƙunshi manyan 'yen siyasa irinsu marigayi shugaba Umaru Yar'Adua, Atiku Abubakar, Baba Gana Kingibe, Rabi'u Kwankwaso, Abdullahi Aliyu Sumaila, Magaji Abdullahi, Dapo Sarumi da Yomi Edu da wasunsu. 
Bola Ahmad Tinubu
 An zabi Bola Ahamad Tinubu a matsayin sanata mai wakiltar sannatan Legas ta yamma a jamhuriya ta uku wadda ba ta yi nisan zango ba sojoji su ka yi juyin mulki tare da rushe mulkin dimokraɗiyya baki ɗaya.
Bayan soke zaben shugaban kasa na "12 ga watan Yuni,a shekarar 1993, sai Tinubu ya zamo daya daga iyayen da su ka kafa gungun kungiyoyin rajin dawo da mulkin dimokradiyya a Najeriya kungiyar da ta shiga wayar da kan 'dan kasa akan nuna rashin goyon bayan mulkin soja da kuma ayyana marigayi Moshood Abiola a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasa da aka soke na ranar.