Wq/ha/Ba Jin

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Ba Jin
Son gaskiya da kuma yin rayuwa ta gaskiya itace dabi'a ta a rayuwa. Ka zama mai gaskiya da kan ka da kuma sauran mutane...

Li Yaotang 李尧棠 (ko kuma Li Feigan; Zi: 芾甘) (Nuwamban 25 1904 – Oktoba 17 2005), marubuci ne dan kasar China; ya yi fice a karkashin sunan rubuce-rubucensa, Ba Jin (巴金, ana kuma rubuta shi a matsayin Pa Chin).

Zantuka[edit | edit source]

  • Bai taba yin jayayya da kowa ba a rayuwar sa, ko da kuwa yaya kuwa suka munanta masa. Ya gwammace ya hadiye hawayen sa, ya kuma kore haushin sa da damuwar sa; zai iya shanye komai ba sai ya yi jayayya da wani ba kai tsaye. Bai kuwa taba tsammani ko da kuwa juriyar sa zata iya zama abun rashin cutarwa ga wasu ba.
    • Dan wasa Chueh-hsin (Juexin), a cikin shirin Family (1931)
  • Nasara ta su ce, ba tamu ba. Bamu sama riba ba daga karyewar tattalin arzikin kasar mu ba. Nasara ba zata kawo mata sa'a ba.
    • The Cold Nights 寒夜 (1947)
  • Kana da taka tunanin kuma nima ina da tawa. Wannan itace gaskiya kuma ba zaka taba iya sauya tawa ba ko da kuwa zaka kashe ni ne.
    • Yayi maganan cikin sauti mai kara a karshen wasan telebijin da aka wulakanta shi a cikin jama'a a People's Stadium of Shanghai, a yayin "Cultural Revolution" (20 June 1968), kamar yadda aka hakayo daga Pioneers of Modern China : Understanding the Inscrutable Chinese (2005) wanda Khoon Choy Lee ya buga