Jump to content

Wq/ha/Ayad Allawi

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Ayad Allawi

Ayad Allawi (Larabci: إياد علاوي. Iyād ʿAllāwī; (an haife shi 31 ga watan Mayu, shikara 1944), ɗan siyasan Iraqi ne. Ya taba zama mataimakin shugaban kasar Iraki daga shekarar 2014 zuwa 2015, firaminista na rikon kwarya daga shekara ta 2004 zuwa 2005 sannan ya kasance shugaban majalisar gudanarwa ta kasar Iraki (Firaministan Iraki na 38) a shekara ta 2003. Ya sake zama mataimakin shugaban kasa a watan Oktoban 2016.

Zantuka

[edit | edit source]

Lallai ina rike da tunanin dan kasar Iraki kuma ni Balarabe ne dan kasar Iraki. Ban yi imani da daular Musulunci a Iraki ba. Na yi imanin cewa daular Musulunci za ta cutar da Iraki da yawa kuma tana iya cutar da yankin. Don haka ina fatan samun wani aiki na kasa a Iraki wanda zai kula da makomar kasar cikin wayewa da zamani da kuma mutunta al'adun Iraki. 18 Oktoba 2005 Ban shirya yin hidima ga mulkin darika ba. Idan har za mu iya cimma buri mai fa'ida, bayyanannen wa'adi na hadin kan kasa, inda ba kome ba idan wani Kurdawa ne ko Balarabe, Sunna ko Shi'a, to a shirye nake in dauki kowane mukami. Dole ne mu gina jihar da ke kan matsayin kare dimokuradiyya. Kuma dole ne hukumomin wannan kasa su sami gurbi ga dukkan 'yan Iraki