Jump to content

Wq/ha/Aminu Bello Masari

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Aminu Bello Masari

Aminu Bello Masari, (an haife shi a ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 1950), dan siyasa ne ɗan Najeriya, kuma gwamna mai ci a Jihar Katsina.Aminu_B_Masari.jpg

Zantuka

[edit | edit source]
  • Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) wanda ya yi mana tsawon rai kuma Ya sa muka ga wannan lamari mai dumbin tarihi.
    • Gwamna Masari: jawabi a ranar rantsar da shi a matsayin gwamnan Jihar Katsina a shekarar 2015.
  • Jama'a maza da mata, a shekara ta (2015) da ta gabata, mun tsaya a wannan farfajiya akan cewa zamu gudanar da harkokin siyasa na wannan jiha na tsawon shekaru 4 da gaskiya da riƙon amana da kuma tsoron Allah, a wannan rana munyi rantsuwa cewa zamuyi amfani da duk wani iko da muke da shi na al'umma da kuma kayan aiki, cikin adalci a wajen maido da katsina zuwa nasarorinta na baya a nan arewa, da kuma ƙasa baki ɗaya.
    • Gwamna Masari: jawabi a ranar rantsar da shi a matsayin gwamnan Jihar Katsina, 2015.
  • Rainin wayau ne a tara talakawa ana yi musu 'yan maganganu.. An san kowa anan ƙasar.. Zaɓe ne tsakanin Haske da Duhu..
    • Aminu Bello Masari
      Gwamna Masari; a wajen kamfen na APC, 2023.