Jump to content

Wq/ha/Amina Titi Atiku-Abubakar

From Wikimedia Incubator
< Wq | ha
Wq > ha > Amina Titi Atiku-Abubakar

Amina Titilayo Atiku-Abubakar, (an haife ta a ranar 6 ga watan Yuni, shekarar ta 1949) yar Najeriya ce mai fafutukar kare Haƙƙin mata da yara kuma daya daga cikin matan tsohon mataimakin shugaban ƙasar Tarayyar Najeriya ne, Atiku Abubakar. Ita ce ta kafa gidauniyar yaki da fataucin mata da cin zarafin yara (WOTCLEF) kuma ita ce ta ƙaddamar da ƙudirin doka mai zaman kansa wanda ya kai ga kafa hukumar hana fataucin mutane ta ƙasa (NAPTIP).

Zantuttka

[edit | edit source]
  • Dole ne mu shugabannin mata su tashi tsaye wajen sake fasalin ƙasarmu ta hanyar samar da ra'ayoyinmu masu kyau don tallafawa manufofin ci gaban Najeriya.
  • Dole ne mu himmatu wajen renon ’ya’ya nagari, kuma ba shakka zamu zaburar da su su yi wa ‘ya’yansu haka. Ta haka ne za mu tayar da hazikan shugabanni masu hankali da tsoron Allah a cikinsu don yin duk abin da ya dace don ci gaban al’ummarmu.