Wq/ha/Aisha bint Abubakar

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > Aisha bint Abubakar

Aisha bint Abubakar[edit | edit source]

A larabci : عائشة‎‎,Ana rubutawa ko karantawa as A'ishah, Aisyah, Ayesha, A'isha, Aishat, Aishah, ko Aisha) takasance ɗaya daga cikin matan annabi Muhammad(S.A.W). A rubutun maguzanci ,don haka sau da yawa sunanta yake ɗaukan taken "Mother of the Believers" (wato uwar muminai)(Alarabci أمّ المؤمنين umm al-mu'minīn). kamar yadda aka faɗi acikin al'kurani mai girma.

Ɗayan sunanta Hadisa .Aisha tana da muhimmiyar rawa a farkon tarihin musulunci , a lokacin rayuwar annabi Muhammadu da kuma bayan mutuwarsa.A hadisin Ahlus-Sunnah,ana zaton A'isha ta kasance mai ilimi da bincike.Ta ba da gudummawa don sake yaɗa sakon annabi Muhammadu tare da yi wa al'ummar Musulmi hidima tsawon shekaru 44 bayan rasuwarsa.Ita kuma ta shahara wajen ruwaito hadisai guda 2210 ba wai akan abubuwan da suka shafi rayuwar Annabi kaɗai ba, har ma da batutuwa kamar gado, hajji da fiyayyen halitta . Hankalinta da iliminta a fannoni daban-daban da suka haɗa da waƙa da likitanci sun sami yabo matuƙa a wajen manyan malamai na farko irin su al-zuhri da dalibarta Urwa bn al-zubayr .

zantuttuka[edit | edit source]

يَغْفُلُونَ عَنْ أَفْضَلِ الْعِبَادَةِ: التَّوَاضُعِ • Mutane ba sa kula da mafi kyawun aikin ibada: Tawali'u An karɓo daga Ibn Abee Shaybah ( 13/360 ) Ibn Hajr ya tattara wannan Athar a matsayin Saheeh =A cikin Hadisin An karɓo daga A'isha (mahaifiyar muminai) cewa: Harith bin Hisham ya tambayi Manzon Allah cewa "Ya Manzon Allah ! Ta yaya ake saukar da wahayi zuwa gare ka ?" Manzon Allah ya ce :" Wani lokaci ta kan bayyana .kamar kararrawar kararrawa wannan nau'in ilhama ita ce mafi wuya daga nan sai wannan yanayin ya wuce bayan na fahimci abin da aka yi wahayi zuwa gare shi , wani lokaci Mala'ika ya zo a siffar mutum yana magana da ni sai na kama duk abin da ya ce." Aisha ta kara da cewa : " Lallai na ga Annabi (S.A.W) ana yi masa wahayi a cikin yini mai tsananin sanyi sai na ga gumi na fita daga goshinsa ( a lokacin da wahayi ya kare ) . Sahihul Bukhari , Vol. 1 , Littafi na 1 , Hadisi na 2

• An karɓo daga Nana A’isha : Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Idan dayanku ya ji barci yana sallah to ya kwanta har barci ya kare domin a cikin sallah alhalin yana cikin barci ba ya sanin ko yana neman gafara ne ko kuwa sharri ne wa kansa."Sahihul Bukhari Juzu'i na 1 , Littafi na 4 , Hadisi na 211.

Nana Aisha : Ni da Manzon Allah (S.A.W) ya kasance muna yin wanka daga tukunya daya a lokacin muna Junub , a lokacin haila sai ya umarce ni da in sanya Izar (tufafin da ake sawa a kasa) yana yi min shagwaba.a cikin I’itikafi ya kasance yana kawo kansa kusa da ni sai in wanke shi alhalin ina cikin haila ya Sahihul Bukhari juzu’i na 1, Littafi na 6, Hadisi na 298 .

• An karɓo daga Aisha ( Matar Annabi ) cewa: Mun yi tafiya tare da Manzon Allah a wata tafiyarsa har muka isa Baida' ko Dhatul-Jaish , abin wuyana ya karye ( ya bace ). Manzon Allah (S.A.W) ya zauna a can yana nemansa , haka kuma mutanen tare da shi.Babu ruwa a wurin sai mutane suka je wajen Abubakar as Siddiq suka ce :shin ba ka ga abin da Aisha ta yi ba ,ta sanya manzon Allah da mutane suka tsaya a inda babu ruwa sai suka sami ruwa. babu ruwa tare da su " Abubakar ya zo alhalin manzon Allah yana barci da kansa a cinyata , sai ya ce mini : " Kun tsare manzon Allah da mutane a inda babu ruwa kuma ba su da ruwa tare da su . sai ya yi min nasiha sannan ya ce da abin da Allah Ya so ya ce ya bugi ni a gefena da hannunsa, ba abin da ya hana ni motsi (saboda zafi) sai matsayin Manzon Allah a kan cinyata, sai Manzon Allah ya tashi lokacin da gari ya waye sai can.Ba ruwa sai Allah ya saukar da Ayoyin Taimiyyah sai suka yi Taimiyya gaba dayansu sai Usaid bin Hudair ya ce : Ya ku iyalan Abubakar ! Wannan ba shine farkon albarkar ku ba .