Wq/ha/Aisha Madawaki
Appearance
Aishatu Madawaki, OFR (an haife ta a shekarar 1951).
Malamar Najeriya ce, kuma yar siyasa. Ita ce mace ta farko farfesa daga tsohuwar jahohin khalifancin Sakkwato a yankin da Musulunci ya mamaye a Arewacin Najeriya,Wanda ya ƙunshi jihar Sokoto a yau da kebbi da kuma zamfara.A shekarar 1999 gwamnatin Attahiru Bafarawa ta nada ta kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma. Madawaki kuma mai fafutukar neman wakilcin, matan Najeriya a fagen siyasa.
Zantuttuka
[edit | edit source]- Domin duk wani ci gaba ya faru, to fa dole ne a sami daidaiton jinsi. [1] Daga na duniya.
- gangamin ranar mata (8 ga watan maris, shekara ta 2017)
- Mata masu zaman lafiya ne, masu juriya, marasa lalacewa da kishin kasa.
- gangamin ranar mata (8 ga watan Maris, shekarar 2017)
- To, na faɗa, lallai abin yana da ƙarfafawa. Idan ka je Jami’o’inmu yanzu na jiha da na tarayya, da kuma kwalejojin ilimi da sauran manyan makarantu yawan mata da ke shiga karatu yana da matuƙar ƙarfafawa. Lallai mata suna ci gaba sosai a yanzu.