Adrienne Maree Brown wacce ake yiwa lakabi da adrienne maree brown (An haife ta a Satumba 6 ga wata, a shekara ta 1978), marubuciya ce, mai fafutuka kuma mai shiryawa. Daga shekarar 2006 zuwa shekara ta 2010, babban darektan Ruckus Society. Ta kuma ƙirƙiri kuma itace darektan League of Young Voters na Amurka.