Wq/ha/Aaliyah
Appearance

Aaliyah Dana Haughton, (An haife ta ne a ranar sha shida (16) ga watan Janairu,a shekara ta alif 1979 - ta mutu a ranar (25) ga watan Agusta ,a shekara ta 2001), takasan ce mawaƙiya ce, sannan kuma ƴar wasan kwaikwayo kuma ƴar talla ƴar ƙasar Amurka.
Zantuka
[edit | edit source]- Na ga (kasidar Vibe din), to amma ban yi tsokaci akan hakan ba don na san ƙarya ne.
- A duk lokacin da mutane suka tambaye ni, ina faɗa musu, "Kalla kada ku yarda duk wannan shirmen. Muna da dangantaka ta kusa to amma mutane sun yi wa hakan mummunan fahimta.
- Aaliyah akan yiwuwar soyayya tsakanin ta ɗan uwanta mawaƙi R. Kelly Disembar shekara ta alif (1994); Christopher John Farley ya hakayo daga cikin Aaliyah: More Than a Woman, p. 47. (2001)
- Yanzu ina da shekaru goma sha bakwai saboda haka na girma a ɓangarori daban-daban, ta fuskar waƙa da sauti
- Tun ina 'yar ƙaramar yarinya na san cewa wannan shi ne abinda nike so in yi. Na fara waƙa ina da shekaru shida (6) saboda haka na sani a yayin da na kai (shekaru) takwas.