Jump to content

Wb/ha/MENENE MAFITAR MU ARAYUWA?

From Wikimedia Incubator
< Wb | ha
Wb > ha > MENENE MAFITAR MU ARAYUWA?

Wata rana ina zaune akasuwa se Allah Ya tunatar dani wani muhim mun abu wanda dama ya jima yana cimun tuwo akwarya,wato shine yadda matasammu suka Sakan-kance tareda shantakewa Rayuwa, wanda hakan ya haifar musu da rashin iya tashi su nemi abinda zasu dogara dashi ta hanyar sana'a. Lallai hakan yakan jawo musu ci baya matuka,saboda yana iya kaisu ga rokon ya'n uwa da makotan su, tareda cewa sunada karfin da zasu tashi suyi sana'a koda kuwa sana'ar karfice,amma sede Kash! ba anan gizan ke sakaba, domin basa iya tabuka komai saboda suna tinanin sunyi Makarantar boko ko Makarantar Allo,seya zamo hakan yana basu matsala ba kadanba, domin basa iya amfanar da kansu balle tallafawa wani, wannan wacce irin hikima ce,alhalin ALLAH ya musu hankali da tinani amma sekaga suna maida kansu kamar DABBOBI, domin dabbobi ne suke zama kullum saidai aciyar dasu,ta wani gurimma dabbobi suna so sufisu amfani Saboda dabbobi ana iya hawa ko kuma ayanka domin aci na mansu. Duk mai hankali inhar ya lurada wannan rayuwar seyaga kawai mutum ya zone agyara zai koma adaukani, saboda mafi yawan masu irin wannan dabi'u basa kulada hakkokin Al'umma Balle su aikata abinda Allan daya halicce su ya daura musu, Allah ya kara shiryar da Al'ummar Annabin Rahama akan daidai. Idan muna bukatar gyara semun tashi tsaye wajen yaki da zaman banza ta hanyar sana'a koda kuwa karamar sana'a ce, domin masu iya magana suna cewa karamar sana'a tafi maula kuma HAKANE,to idan har mun fahimci hakan ya kamata mudena ruduwa da wani karatun da mukayi murun gumi sana'a duk kankan-tarta,muru-fawa kammu asiri, domin Mahimmanci sana'a har anna bawan Allah sunayin sana'a.. Malam Abu Shareefa Pkm Malam Abbapkm Almajirin Sheik Mustafha