Wq/ha/hauwa maina

From Wikimedia Incubator
< Wq‎ | ha
Wq > ha > hauwa maina

Hauwa Maina'’' yar wasan Kannywood ce kuma furodusa wadda ta fito a cikin fim din Sarauniyar Zazzau. Ta rasu ne sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba a asibitin Kano a ranar 2 ga Mayu, 2018.

Zantuttuka[edit | edit source]

  • Akwai banbanci tsakanin yin wasan kwaikwayo a Nollywood da Kannywood. A Kannywood kullum muna tabbatar da cewa ba mu aikata abin da zai saba wa addininmu ko al’adunmu ba, amma a Nollywood suna sumbata, runguma, da yin duk wani abu na batsa. Wasu daga cikin ayyukansu suna iya yin fina-finan manya cikin sauƙi.
  • Amma duk da haka ina son a tuna ni da Hauwa Maina 'yar Biu wadda aka haifa a Kaduna a matsayin musulma kuma na bauta wa Allah a iyakar sanina kuma ina fatan shiga aljanna a duk lokacin da na amsa kiran magabata na.