Wq/ha/Kim Campbell
Appearance

Avril Phaedra Douglas "Kim" Campbell (An haife ta a ranar 10 ga Maris, 1947) ita ce ‘yar siyasa, diplomasiyya, lauya, da marubuciya daga ƙasar Kanada. Ta rike mukamin Firayim Ministan Kanada na 19 daga ranar 25 ga Yuni zuwa 4 ga Nuwamba, 1993. Campbell ce mace ta farko kuma ita kaɗai da ta taɓa zama Firayim Ministan Kanada har yanzu. Kafin ta zama Firayim Minista daga jam’iyyar Progressive Conservative (PC), ita ce mace ta farko da ta rike mukamin Ministan Shari’a a tarihin Kanada da kuma mace ta farko da ta zama Ministan Tsaro a cikin ƙasar memba a kungiyar NATO.
- Abubuwan da na yi sun bambanta, amma dabi’u da abubuwan da nake so suna nan dai-dai.
- [1] Hira da Helen Farrell
- Abin bakin ciki shi ne cewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi daɗi a rayuwa shi ne raira waka tare da wasu, amma kuma yana ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi saurin yada ƙwayar cuta.
- [2] Akan yadda take jin daɗin wakarta
- “Gwamnatoci ba koyaushe suke zama mafiya kwarewa ba wajen gano cututtukan tattalin arziki da bayar da maganin da ya dace.”
- [3] Akan gwamnati
- Ikon gaskiya ne kuma wani zai mallake shi. Don haka, idan za kayi amfani da shi cikin gaskiya da kuma don amfanin kasa, me ya sa ba kai ba? Kuma me ya sa ba ni ba?
- [4]
- Ba wariyar mata na cewa ‘Ba ma son mata’ in ji ta. “Wariyar da nake nufi ita ce wadda ke sa a auna ki da wani mizani dabam, ba a ba ki fifiko ko amincewa da gaggawa, kuma ana yin aiki da zato ke ba ki dace ki kasance a wurin ba.”
- [5] Ta bayyana ‘wariyar mata’ da ‘muna-muna’.
- Yayin da shekaru ke wucewa kuma babu wani da ya sake yin haka, ina Jin nauyi na tunatar da mutane ma’anar a zabe ka a matsayin shugaban jam’iyyar da ke mulki. Amfanin hakan shi ne don karfafa gwiwar wasu su yi mafarkin kaiwa wannan matsayi.
- [6]
- Tabawa mutum jiki ba tare da yardarsa ba laifi ne na fyade. Kuma duk wanda yake yin hakan, wanda yake tunanin yana da hakkin yin hakan, wanda yake ganin yana iya yin hakan saboda yana da suna ko mashahuri ne, wannan dai halin macuci ne.
- [7] Campbell ya gaya wa kamfanin gidan Rediyon Kanada
- Ya fitar da maganganun kin mata masu yawa yana boye su a matsayin adawa da gyaran halayen siyasa. Barin mutane suna fadin mugayen ra’ayoyi na wariyar mata yana da matukar hadari kuma abin damuwa ne kwarai da gaske.