Wq/ha/Bibi Titi Mohammed
Appearance

Bibi Titi Mohammed (June 1926 – 5 November 2000) ta kasance ‘yar siyasar Tanzaniya ce kuma mai fafutukar hakki. An fara daukan ta a matsayin mai yakin neman ‘yancin kai kuma ta goyi bayan Shugaban kasar Tanzaniya na farko Julius Nyerere. Bibi ta kasance memba ta jam’iyyar Tanganyika African National Union (TANU), jam’iyyar da tayi yaki don samun ‘yancin kan Tanzaniya kuma ta rike mukamai na Minista da dama. A cikin watan Oktoban 1969 an yanke mata hukunci don cin amanan kasa, sannan bayan shekaru biyu a kurkuku an yafe mata karkashin afuwan shugaban kasa.
Zantuka
[edit | edit source]- Mata na bukatan mutuntawa, tallafawa da kuma dama ba wai tausayawa ba.