Wq/ha/Balaraba Ramat Yakubu
Appearance
Balaraba Ramat Yakubu kwarariyar marubuciyar littafan Hausa ce da ake wa laƙabi da littattafan soyayya. An kuma haife ta a cikin birnin Kano a shekarar 1959[1] . Tana daga ƙalilan marubuta da aka fassara littafinta zuwa harshen Turanci. Rubuce - rubucen ta sun fi bada muhimmanci akan zamantakewar aure da kuma gwagwarmayar mata a rayuwar Hausawa, musamman tauye Haƙƙin mata da mazan Hausawa kan yi, zamu ga haka a littattafan ta kamar Budurwar zuciya da mashahurin littafin ta Alhaki kuikuyo ne.
Zantuka.
[edit | edit source]- Talla masifa ce ga mata.
- [1] Balaraba ta zanta haka a hirar ta da jaridar Aminiya.
- Mu musulmai ne kuma muna da dokokin addinin mu na Musulunci a kan sha'anin aure. Amma a wasu lokuta al'adun mu suna maye gurbin addinin kuma al'adu da addini ba ɗaya bane. Ina yaƙi saboda ina so na nuna cewa addini da al'adu suna da bambanci.
- We are Muslims and we have rules in Islam for marriage and so on. But sometimes, our culture dominates the religious dictates and culture and religion are different. So, I fight because I want to stress that culture and religion are different. Probably that is why I'm called a controversial writer.
- ...Ina taɓa maudu'in da wasu marubuta suke tsoron yin rubutu a kan su. A baya, wasu dattawa kamar tsararrakin mahaifiyata suna tunanin cewa mijin su shine na biyu bayan Ubangijin su amma sai na wayar da su cewa mijin su kamar tsaran su ne.
Manazarta
[edit | edit source]- ↑ Femke van Zeijl, "From illiterate child bride to famous Nigerian novelist", Al Jazeera (Features), 8 March 2016.