Wq/ha/Alkur'ani
Alqur'ani Littafin Allah Subhanahu wataala,
al- qur'ani a zahirin ma'anar sa shi ne 'karatun') kuma Ƙur'ani ko Al Kur'ani na romanized shi ne nassin addinin musulunci na tsakiya wanda musulmai suka yarda da zama wahayi daga Allah. An tsara shi a cikin surori 114 wanda ya ƙunshi ayoyi da 6666, Baya ga muhimmancinsa na addini ana kallonsa a matsayin mafi kyawun aiki a adabin Larabci, kuma ya yi tasiri sosai a harshen Larabci,
Zantuttuka
Surar 1 : Budewa (Al Fatiha)
¹ Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
2 Gõdiya ta tabbata ga Allah, Majiɓincin tãlikai.
3 Mafi rahamah, Mafi jin ƙai.
4 Mai Mulki a ranar sakamako. 5 Kai muke bauta wa, kuma taimakon ka muke nema.
6 Ka nuna mana hanya madaidaiciya.
7 Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima a kansu, ba waɗanda kayi fushi dasuba kuma ba ɓatattu ba.
Na Larabci
1 بسمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
2 الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَلَمِينَ
الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ 3
مُلِكِ يَوْمِ الدِّينِ 4
إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ 5
اهْدِنَا الصِّرُّطَ الْمُسْتَقِيمَ6
صِرُّطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ 7
•Al Qur'an, Sura ta Farko 1:1-7