Wq/ha/Aishatu Madawaki
Appearance
Aishatu Madawaki', OFR(An haife ta a shekara ta alif 1951) ƴar jami'ar Najeriya ce kuma ƴar siyasa. Ita ce mace ta farko farfesa daga tsohuwar Jahohin Sokoto (wanda ya haɗa da a yau Jahar Sokoto, Jahar Zamfara da kuma Jihar Kebbi), yanki ne da musulunci ya mamaye a Arewacin Nijeriya. A shekarar 1999, gwamnatin Attahiru Bafarawa ya jagoranci naɗa ta kwamishiniyar harkokin mata da cigaban jama'a. Madawaki kuma mai fafutukar neman, wakilcin matan Najeriya a fagen siyasa.
Zantuka
[edit | edit source]- Domin wani ci gaba ya faru, dole ne a sami dai-daiton jinsi.
- Mata masu zaman lafiya ne, masu juriya, marasa lalacewa da kishin kasa.
- Ba kawai a ba ta ilimi ba, a kuma koya mata ƙwarewa da za su ba ta damar ƙarfafawa kanta. Kada ilimin ya tsaya kawai a rubuce ko a nazari, a tabbatar da cewa tana samun ilimin aiki da hannu (na zahiri) ma.
- Don haka batun mayar da mata baya abu ne na da, yanzu mata sun waye sosai, sun san cewa su ma mutane ne, Allah ne ya halicce su kamar kowa.
- Idan za mu bi cancanta, muna da mata masu hankali da azama da jajircewa waɗanda ke da natsuwa kuma za su iya aiwatar da kowanne aiki a kowane lokaci.
- Ba wai kawai samarwa mace damar samun ilimi na farko ba ne, amma abin da zai faru bayan hakan. A ba ta ƙwarewa da za su ba ta damar ƙarfafa kanta, ba wai ta tsaya kawai ga samun ilimi ba. A bar ilimin shima, amma kada ya tsaya ne kawai a ɓangaren koyarwa ta baki, a samu ɓangaren amfani da shi a aikace.
- Idan addininka ya ba ka iko, dama da izinin neman ilimi a duk inda za ka same shi, to menene ke hana ka? Matsalar kawai ita ce hali ko dabi’a, kuma dole ne mu magance hakan mu sauya.
- Akwai ƙalubale da ba za a iya shawo kansu ba, kuma akwai ƙalubalen da za a iya shawo kansu. Saboda haka, ina ganin cewa ƙalubale abu ne mai kyau a rayuwar mutum domin ƙalubale su ne ke gina mutum.