Wq/ha/Aishatu Dahiru Ahmed
Appearance
Aishatu Dahiru Ahmed (an haife ta 11 ga watan Agusta, shekara ta 1971), wacce aka fi sani da Aisha Binani, ‘yar siyasar Najeriya ce kuma ‘yar kasuwa wacce ta kasance Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya daga shekara ta 2019 zuwa shekara ta 2023. A ranar 30 ga watan Maris, shekara ta 2020, Majalisar Masarautar Adamawa ta nada ta Gimbiyar Adamawa.
Azanci
[edit | edit source]- Nagartattun mutanen Garkiɗa za su ci gaba da tunawa da kyakkyawan Sanata. Majalisar dattijai tana sane da cewa a ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar 2020, wata kungiyar tada kayar baya ta kai hari ga mutanen Garkida, gari mai zaman lafiya a karamar hukumar Gombi a gundumar Adamawa ta tsakiya. Maharan dauke da manyan motoci sama da bakwai da babura da dama sun kai hari garin da misalin karfe 7:00 na dare, inda suka kona gine-gine da dama. Kazalika sanin cewa sojoji uku ne suka mutu a wannan mummunan harin. An kone ko kuma lalata kadarori na miliyoyin Naira da suka hada da asibitocin gwamnati, makarantu, cibiyoyin sadarwa, ofisoshin ‘yan sanda, motocin bas, motoci, shagunan abinci, kadarori masu zaman kansu na mutanen Garkiɗa. Damuwa da cewa rikicin Garkiɗa wanda yayi sanadiyar salwantar rayuka da dukiyoyi yan tada kayar bayan sun shirya yin ma'anar addini duba da cewa an kona majami'u da gidajen wasu fitattun 'yan asalin kasar. Da nufin ruguza ginshikin zaman lafiya tsakanin al'ummar Garkiɗa da jihar Adamawa baki daya...
- Sanata Aishatu Dahiru Ahmed ta gabatar da kudiri kan harin da 'yan ta'adda suka kai a Garkiɗa. Majalisar Dattawan Najeriya (shafin Facebook) 25 ga watan Fabrairu, shekara ta 2020.