Wq/ha/Aisha Sekindi
Appearance

Aisha Sekindi (An haife ta a ranar 4 ga watan Disamba, 1970) malamar makaranta ce kuma ‘yar majalisa daga Uganda. Daga watan Fabrairun shekarar 2022, tayi aiki a matsayin Karamar Ministar Ruwa ta Uganda, kuma wakiliyar mata ta gundumar Kalungu a majalisar dokokin Uganda ta goma sha daya. Ta maye gurbin Hon. Ronald Kibuule wanda ya mika ofis a watan Yulin shekarar 2021. Ta kuma rike wannan matsayi a majalisa ta goma ta Uganda. A siyasance, tana da alaƙa da National Resistance Movement (NRM), a ƙarƙashin wannan jam’iyya ta tsaya takara a zaɓen gama gari na shekarar 2016, inda ta yi nasara kan Aisha Naluyati Waligo na jam'iyyar Democratic Party (DP) ta Uganda.
Zantuka
[edit | edit source]- Mu daina mai da hankali kan bambancin jam’iyyun siyasa, sai dai mu mayar da hankali kan jin daɗin jama’armu. Kada mu bari siyasa ta raba kan mu bisa ga jam’iyya.
- Bambancin ra'ayin siyasa bai kamata ya hana ku bin babban manufa ta ci gaban kasa da zaman lafiya ba.
- Mu a matsayin shugabannin siyasa mun taka rawa sosai wajen rikita al’umma, kuma dole ne hakan ya sauya. Jam’iyyar NRM ta zo da manufa ta haɗa kan al’umma ba tare da la’akari da addininsu, al’adunsu ko dangantakar siyasa ba.
- Daga ra'ayoyin da muka samu, mahalarta taron suna da ra'ayi mai kyau sosai game da sakonmu na ƙarfafa soyayya ga ƙasa. Wannan shi ne abin da ya dade babu a cikinsu saboda shawarwari marasa kyau daga wasu shugabanni. Sakamakon haka, wasu sukan ƙare da ƙin ƙasarsu.
- Zai iya yiwuwa mu ɗauka cewa matasa ba sa goyon bayan gwamnati, amma watakila kuskurarmu ne domin ba mu kusanta da su ba. Sakamakon haka, albarkatun da aka tanada domin taimaka musu sau da yawa suna ƙarewa a aljihun 'yan technocrats.