Wq/ha/Aisha Salaudeen
Appearance
Aisha Salaudeen (An haife ta a ranar 26 ga watan Satumba, shekarar 1994) 'yar Najeriya ce 'yar Jarida, ɗan gwagwarmayar kare hakkin mata (feminist), mai shirya shirye-shirye kuma marubuciya wacce ke aiki da CNN a halin yanzu. A watan Nuwamba na shekarar 2020, an ba ta lambar yabo ta Future Awards Africa Prize for Journalism saboda irin ƙoƙarinta wajen rufe labarai daga nahiyar Afirka.
Zantuka
[edit | edit source]- Akwai wani mizani da ake dora mata a kai wanda ya fi na maza. Me ya sa idan mace ce ake ɗaukar lamarin da girma sosai, har ya zama kamar abin ban haushi da ɗaure kai?
- Kafofin sada zumunta sun kasance masu amfani domin za ka iya amfani da su wajen samun bayanai domin labarai, kuma za ka iya amfani da su wajen tattara bayanai.
- Duniya tana ta canzawa a koyaushe, kuma dole ne ka nemo hanya mafi kyau domin ba da labarinka. Wani lokaci rubutu kaɗai ya isa, amma wani lokaci kuma za ka iya juya shi zuwa podcast ko sigar sauti, duk ya danganta da abin da labarin ke bukata.
- Podcasting har yanzu sabuwar fasaha ce da mutane ke fara sabawa da ita, musamman a Afirka. Podcasting yana da wahala domin har yanzu mutane da dama na ganin tamkar rediyo ne, kuma kana bukatar haɗin intanet domin sauraron kowanne shiri.
- Dole ne ka kasance mai bude zuciya. A farkon farawa, za ka fara yin ayyukan da ba ka jin daɗinsu sosai, domin kana bukatar samun kwarewa da fasahohi da yawa gwargwadon iko.
- Idan kana ikirarin cewa kana ba da labaran mata 'yan Afrika amma ba ka rubuta ko bayyana munanan abubuwan da suka faru da su ba, to hakan yana nuna baza ka yi gaskiya a cikin rahotanninka game da mata ba, domin waɗancan munanan abubuwan sune gaskiyar rayuwa ga mata da dama.
- Gaba ɗaya, kasuwancin kafafen yaɗa labarai ba'a Najeriya kaɗai ba, har ma da Afrika gaba ɗaya yana da wahala. Kafafen yaɗa labarai har yanzu ba su gano ingantaccen hanyar samun kuɗi ba.