Wq/ha/Aisha Rimi
Appearance
Aisha Rimi daga Jihar Katsina take a Arewacin Najeriya. Tana daga cikin abokan harkan da suka kafa kamfanin Africa Law Practice (ALP NG & Co), wani kamfani na dokokin kasuwanci a Najeriya. Ta kammala karatunta na digiri na farko (LLB) da digiri na biyu (LLM) a fannin lauya daga Jami’ar Buckingham da ke Ingila(England).
Zantuka
[edit | edit source]- Ba kawai mun zo ne domin tallatawa ba, har ma domin saukaka abubuwa. Idan mun yi nasara, Najeriya ma za ta yi nasara. Na yi girman da bai kamata in tafi ba, kuma ba zan iya zuwa ko’ina ba.
- Ina da babban rabo daga tarbiyya ta, ilimi, ƙwarewa da kuma goyon bayan iyalina. Na taso a gida na musulmi mai ra'ayin daga Arewa, inda iyayena duka kwararru ne masu nasara a rayuwa. Tun muna ƙanana, iyayenmu suna ƙarfafa mana gwiwa, maza da matan mu, mu nemi ilimi kuma suna ba mu goyon baya a kowanne zaɓin sana'a da muka yi. Sun koyar da mu cewa ilimi da aiki tukuru su ne mabuɗin nasara.
- Aisha spoke about her upbringing New Telegraph
- Ba ina nan domin in ƙirƙira abin da tuni aka riga aka ƙirƙira bane. Taya tana nan, abinda ya rage kawai shi ne mu sa tayi aiki. Dole ne mu shafa mata mai, mu gyara ta yadda ya kamata. Dole ne mu sa duk abin da ya kamata domin wannan injin ya yi aiki. Domin kamar yadda na faɗa tun da farko, idan mun yi nasara, Najeriya ta yi nasara, kuma za mu kasance ɓangare na wannan labarin nasara.
- Aisha was optimistic about her role Naira Metrics